Mahara sun sake kone ofishin Hukumar Zabe ta Kasa INEC a Jihar Imo da ke Kudancin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kone ofishin Hukumar da ke yankin Okwudor a Karamar Hukumar Njaba da safiyar ranar Lahadi.
Wannan lamari na zuwa ne bayan sa’a 24 da aukuwar makamancinsa, inda aka kone ofishin ’yan sanda na Atta da kuma wasu kotuka biyu da ke yankin Karamar Hukumar.
Jami’ar Hulda da Al’umma ta Hukumar, Emmanuella Opara, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ana iya tuna cewa, a makon jiya ne Hukumar INEC ta bayyana fargaba kan hare-haren da ake ci gaba da kai wa ofisoshinta a garuruwa da dama na kasar.
Hukumar ta bayyana fargaba kan makomar Babban Zaben kasa na 2023, inda ta ce an kai wa ofisoshinta 41 hari cikin shekaru biyun da suka gabata.