Wasu ’yan bindiga sun far wa wani gida a yankin Eteh-Okofi da ke Karamar Hukumar Koton Karfe ta Jihar Kogi inda suka sace wasu ’yan mata uku ’yan uwan juna.
A yayin zantawar Aminiya da wani dan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su kuma ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya faru tun da duku-dukun ranar Talata.
- Gobara ta yi ajalin ’yan uwan juna hudu a garin Bida
- An fara yi wa fursunoni rigakafin cutar Coronavirus
- Sarkin Kano ya umarci jama’a su karbi allurar rigakafin coronavirus
Ya ce maharan na dira gidan kai tsaye suka afka uwar dakan da ’yan matan ke kwance suka tashe su sannan suka tisa keyarsu cikin dokar daji.
“Tamkar a mafarki motsin maharan ya sanya daya daga cikin ’yan uwan matan ya farka daga bacci, kuma yana bude kofa domin ganewa idanunsa abin da ke faruwa sai ’yan bindigar suka fara harbi a cikin iska,” a cewarsa.
Ya ce a yanzu maharani sun tuntubi ’yan uwan wadannan mata inda suka nemi a biya su naira miliyan dari a matsayin kudin fansa, lamarin da ya ce har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.
Shugaban Karamar Hukumar ta Koton Karfe Isa Abdulkarim, ya inganta rahoton sai dai ya ce ba ya da wani cikakken bayani a kan aukuwar lamarin.
Yayin da aka nemi jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Williams Ayah, bai amsa kiran wayarsa ba sannan bai bayar da amsar sakon kar ta kwana da aka aike masa ba.