✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace uwa da ’ya’yanta hudu a Kaduna —’Yan sanda

’Yan sanda a Jihar Kaduna sun tabbatar cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da wata uwa da ’ya’yanta hudu a Karamar Hukumar Chikun ta jihar.…

’Yan sanda a Jihar Kaduna sun tabbatar cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da wata uwa da ’ya’yanta hudu a Karamar Hukumar Chikun ta jihar.

Masu garkuwa da mutanen sun yi dirar mikiya a gidan matar suka tafi da ita da ’ya’yanta ne a unguwar Sabon Tasha kafin wayewar garin ranar Asabar.

Kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed ya ce an yi garkuwa da su ne a daidai lokacin jami’an tsaro ke kokarin dakile wasu masu garkuwa a mutane a unguwar.

Ya ce Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta zage damtse domin kubutar da mutanen cikin aminci.

Ya ce da farko sun samu kiran neman agaji daga unguwar Sabo GRA a lokacin da masu garkuwar ke nema kutsawa gidan amma ’yan sanda suka fatattake su.

Abin takaici kuma ashe an kai hare-haren ne a lokaci guda, aka tafi da matar da ’ya’yanta.

Ya ce tuni suka fara bincike kan lamarin.