✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace mutum 60 suna tsaka da ibada a Kaduna

Hayab ya ce katse layukan sadarwa ya haddasa jinkirin bullar rahoton sai a yanzu.

’Yan bindiga sun sace akalla mutum 60 tare da hallaka mutum guda yayin wani hari da suka kai kan wani coci a Jihar Kaduna.

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN reshen jihar, Rabaran John Hayab ne ya tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin.

Rabaran Hayab ya ce shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne a Cocin Emmanuel Baptist da ke Kauyen Kakkau Daji a Karamar Chikun ta Jihar Kaduna.

A cewarsa, lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, yayin da mutane ke tsaka da gudanar da ibada, sai dai katse layukan sadarwa ya haddasa jinkirin bullar rahoton sai a yanzu.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya inganta rahoton sai dai bai fayyace adadin mutanen da aka yi awon da gaba da su ba.

Aruwan ya kuma bayyana cewa wani Yusuf Dauda shi ne mutumin da karar kwana ta cimmasa yayin harin.

A bayan nan wasu rahotanni sun bulla cewa ’yan bindigar mutum sama da 100 suka sace, sai dai Rabaran Hayab mutum 60 kacal ya iya bayar da tabbaci a kai.