Ana fargabar ’yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan kamfanin gine-gine su hudu a garin Tashar Yari da ke Karamar Hukumar Makarfi ta Jihar Kaduna.
Wasu mutum biyu kuma sun ji raunuka kuma yanzu haka suna samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya.
- DSS ta cafke Abdulaziz Yari
- An bukaci Amurka ta hana Abba izinin shiga kasarta saboda rushe-rushe a Kano
An kai harin ne ranar Asabar.
A cewar wata majiya a yankin, maharan sun kewaye ginin da ma’aikatan ke zaune ne, sannan suka yi awon gaba da mutanen.
Lamarin ya faru ne a kan babban titin Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano, inda ma’aikatan ke cikin masu aikin gina titin.
Majiyoyi da dama a garin Makarfi sun tabbatar da faruwar harin, ciki har da wani shugaban al’umma da ya nemi a sakaya sunansa.
A cewar shugaban, maharan sun isa yankin ne cikin dare lokacin ana ruwan sama, inda suka kai wa mutanen hari ba tare da wata matsala ba.
Ya kuma ce, “An sace mutum hudu, wasu biyu kuma sun samu raunuka, kuka nan take aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.”
Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Mohammed Jalige, ya ci tura saboda bai amsa kira wayarsa ba.
Kazalika, har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai amsa sakon kar-ta-kwanan da aka tura masa ba.