✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace mahaifiyar Samson Siasia

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi awon gaba da mahaifiyar kocin kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa…

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi awon gaba da mahaifiyar kocin kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) Samson Siasia, Madam Ogere Siasia a ranar Talatar da ta wuce, kamar yadda kafar samar da labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito.
Rahoton ya ce bata-garin sun sace tsohuwar ce ’yar kimanin shekara 72 a gidanta da ke kauyen Odoni a karamar Hukumar Sagbana na Jihar Bayelsa da sanyin safiyar Talata, 17 ga wannan wata da muke ciki.
A lokacin da yake tabbatar da labarin ga ’yan jaridu, Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Bayelsa ASP Ansinin Butswat ya tabbatar da aukuwar wannan labari, inda ya ce tuni iyalanta suka tuntubi hukumarsa don sanar da su halin da ake ciki.
Kamar yadda rahoto ya nuna, ’yan bindigar sun isa gidanta ne tun a cikin dare inda suka labe kafin daga bisani suka kutsa cikin gidan a lokacin da mafi yawa daga cikin mutanen kauyen suna barci kuma suka yi awon gaba da ita a kan babur.
Sai dai ya zuwa hada wannan rahoto ba a samu wani bayani daga wajen wadanda suka sace ta din ba.  Amma alamu sun nuna sun yi haka ne don su karbi makudan kudi daga wajen iyalanta.
Tuni Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta roki wadanda suka yi garkuwa da ita su yi gaggawar sakinta ba tare da gidanya wasu sharudda ba.
Wannan garkuwa da aka yi da mahaifiyar Samson Siasia, ba karamin cikas zai kawo wa kocin ba musamman a wannan lokaci da yake shirin tafiya da kungiyar U-23 gasar cin kofin Afirka na ’yan kasa da shekara 23 da za a fara kwana nan.