’Yan bindiga sun sace mahaifin mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kwali da ke babban birnin tarayya, Mohammed Yakubu da wasu mutum shida.
Rahotanni sun ce maharan sun harbe wani mutum, sannan suka yi awon gaba da wata mai juna biyu da wasu mutum biyar a kauyen Yewuti da ke karamar hukumar.
Aminiya ta ruwaito cewa mahara sun taba kai hari kauyen a ranar watan Afrilu, suka sace mutum 29.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, wani mazaunin garin Ibrahim Danjuma ya ce da misalin karfe 12 na safe maharan dauke da bindigogi kirar AK-47 suka mamaye wasu gidaje uku ciki har da na mahaifin mataimakin shugaban, suka tafi da shi tare da wasu mutane shida.
Ya kara da cewa, “’yan bindigar sun harbe daya daga cikin mutanen kauyen, Hussaini Kure, wanda ya yi yunkurin tserewa.”
Basaraken yankin, Etsu Yewuti, Mohammed Isyaku, wanda ya ce al’ummar yankin sun firgita da harbi da ’yan bindigar suka yi ya roki mahukunta da su taimaka wa talakawansa wajen gain jami’an tsaro sun kubutar da wadanda aka sace.
Ya ce, “Karo na uku ke nan wannan abin bakin ciki da damuwa ke faruwa a al’ummarmu. Ina kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su kawo mana agaji domin ceto wadanda aka sace ciki har da wata mace mai juna biyu.”
A halin da ake ciki ’yan bindigar sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 30.”
Kakakin ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, ta ce tana coci lokacin da aka kira ta game da faruwar lamarin.