Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa mutane hudu a kauyan Hayin Kinini da ke yankin Kakangi na Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
Shugaban Kungiyar Cigaban Masauratar Birnin Gwari, Ishaq Kasai, ya shaida wa Aminiya a Kaduna cewa ’yan bindigan sun yi garkuwa ne da wani magidanci da matarsa da ’ya’yansa biyu a cikin dare.
Al’amarin ya bayyana lamarin na ranar Talatar nan da ta wuce, inda ’yan bindiga suka kai hari a wani gida da ke wajen kauyen a matsayin abin takaici.
Shugaban kungiyar ya ce mafi akasarin mazauna kauyen ba su san ’yan fashin dajin sun shiga gidan ba, saboda maharan ba su yi harbi ba.
- Sojoji sun kwato mutane daga maboyar ’yan bindiga a Kebbi
- An ci gaba da kashe-kashe duk da dokar hana fita ta sa’a 24 a Filato
“Har sai da mahifiyar magidanci ta ziyarci gidansa, bayan ta lura shi da ’ya’yansa ba su zo gidanta domin gaishe ta da safe ba.
“Hakan ya sa ta gano cewa an sace shi da iyalaninsa a cikin dare, saboda gidansa na gefen gari ne,” in ji Ishaq Kasai.
Ya kuma koka game da karuwar garkuwa da mutane a yankin karamar hukuma, inda ya bukaci gwamnati ta kai masu dauki.
Wakilinmu ya kira kakakin rundunar ’yan Sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, domin samun karin bayani, amma jami’in bai amsa wayarsa ba, kuma bai ba da amsar sakon tes da aka aika masa a kan batun ba.