’Yan bindiga sun sace limamin Cocin St. Mary da ke Sarkin Pawa, hedkwatar Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja, Rabaran Fada Leo Raphael Ozigi da wasu mutum 44.
Rahotanni sun ce an sace su ne bayan wani hari da ’yan bindigar suka kai da yammacin ranar Lahadi.
- Maryam Yahaya ta dawo fim ka’in da na’in
- Mahaifin almajirin da aka yi wa kaca-kaca da duka ya ce bai san dansa na Kano ba
Wakilinmu ya gano cewa an sace limamin ne lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Gwada daga Sarkin Pawa, lokacin da suke tsaka da kwasar mutane.
Sakataren Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen Jihar Neja, Fasto Raphael Opawoye, ne ya tabbatar da sace limamin Cocin ga wakilinmu.
“Am sace Rabaran Dokta Leo Raphael Ozigi lokacin da yake hanyarsa ta dawowa daga Gwada zuwa Sarkin Pawa, bayan kammala ibada ranar Lahadi,” inji shi.
Shi kuwa Sakataren Karamar Hukumar ta Munya, James Jagaba, ya bayyana sabbin hare-haren da ake kai musu tun ranar Asabar a matsayin abin takaici.
Ya ce yanzu kusan daukacin Karamar Hukumar na cikin mawuyacin hali.
Wani mazaunin yankin, Shehu Abubakar, ya shaida wa wakilinmu cewa mutum 44 da aka sace na cikin wadanda ke kokarin komawa muhallansu daga sansanonin ’yan gudun hijira ranar Asabar.
“Yanzu yadda suka ga dama suke yawo, sai cin karensu suke yi ba babbaka.”
Ya ce tun ranar Asabar ’yan bindigar ke ta sintiri a kan hanyar Sarkin Pawa zuwa Gwada hankalinsu kwance, tare da shanun da suka kwace daga kauyukan da suka kai wa hari.