Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki kauyen Tafoki a Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da kanwar Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin jihar, Shehu Dalhatu Tafoki.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho ga wakilinmu, Tafoki, ya ce kanwar tasa da aka yi garkuwa da ita ’yar makarantar sakandare ce kuma an kusa daura aurenta.
SAURARI: Yadda Kwaya Ke Kashe Aure da Ma’aurata:
- Rufe kasuwanni da makarantu da hanyoyin sadarwa ba maslaha ba ne – Dattawan Arewa
- NDLEA ta kama mai yi wa kasa hidima da ke safarar miyagun kwayoyi
“Tabbas ’yan bindiga sun yi garkuwa da kanwata da sanyin safiyar ranar Lahadi.
“Sun farmaki kauyen da misalin karfe 1 na dare inda suka wuce kai tsaye zuwa gidan mai gari, wanda shi ne gidan iyayenmu sannan suka sace kannena mata biyu.
“A kan hanyarsu ta zuwa daji sun hadu da ’yan banga inda suka yi harbe-harbe a tsakaninsu har daya daga cikin yaran ta tsere ta dawo gida dayar kuma suka tafi da ita,” inji Mataimakin Shugaban Majalisar.
Ya ce har ya zuwa yanzu ’yan bindigar ba su nemi iyalansu ba.
Wannan na zuwa ne awanni kadan da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da mata da ’ya’yan dan majalisar dokokin jihar, Dokta Ibrahim Kurami a kauyen Kurami da ke Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina.