✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace dan uwan Ministan Noma Sabo Nanono

Wasu ’yan bindiga da ba a san daga inda suka fito ba sun sace wani dan uwan Ministan Noma na Najeriya, Alhaji Sabo Nanono, a…

Wasu ’yan bindiga da ba a san daga inda suka fito ba sun sace wani dan uwan Ministan Noma na Najeriya, Alhaji Sabo Nanono, a daren Lahadi.

Maharan sun yi awon gaba da dan uwan Ministan mai suna, BabawuroTofai kamar yadda rundunar ’yan sandan jihar Kano ta bayar da tabbaci.

Jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, shi ne ya yi karin haske game da faruwar lamarin, sai dai ya bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin.

A baya-bayan nan an samu yawaitar ayyukan ’yan bindiga na sace-sace da garkuwa da mutane musanman a yankin Arewacin Najeriya, ta yadda kusan kullum ake kara samun yawaitar labaran garkuwa da mutane ba dare ba rana.

Jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara na daga cikin garuruwan da abun yafi shafa da wasu sassa na Kudancin kasar nan, inda a ranar Lahadi 15, ga watan Nuwamban da muke ciki masu garkuwa da mutane suka kashe akalla mutane 15 a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

 

%d bloggers like this: