✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa siyasa a daukar jami’an tsaro, inji Zulum

Ya ce dole a cire siyasa da daukar jami'an tsaro sannan a bar batun ’yan sandan jihohi.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi zargin sanya siyasa a wajen daukar sabbin jami’an tsaro a Najeriya.

Zulum ya ce hakan ce ta sanya sha’anin kula tsaron Najeriya ya kare a hannun mutanen da aikin yi kawai suke nema domin samun albashi, ba masu kishin kasar ba.

“Babbar matsalar ita ce tun a wurin daukar ma’aikatan; Wadanda ake dauka aikin soja ko dan sanda da sauran hukumomin tsaro aiki kawai suke nema, yawancinsu saboda sun gaji da zaman kashe wando ko sun rasa wani aikin.

“Idan aka lura za a ga wadanda suka shiga aikin shekara 20 kafin yanzu suna taka rawar gani, amma wadanda ake dauka yanzu aikin yi kawai suke nema, shi ya sa ba sa nuna hazaka ko kishin kasa.

“Yanzu har gurbin wadanda za a dauka aiki ake ware wa gwamnoni da ministoci da manyan jami’an gwamnati idan aka tashi daukar jami’an tsaro.

“Sannan idan suka kawo yaran nasu babu wata jarabawa da ake musu domin tabbatar da sun cancanta. Yanzu dai an siyasantar da daukar aikin soja da na dan sanda,” inji shi.

– Abin da ya kamata

A jawabin nasa a Cibiyar Koyar da Dabarun Aiki, (NIPSS) da ke Kuru a Jihar Filato, ranar Laraba, Zulum ya ce, “Dole sai an yi abin da ya dace, in ba haka ba, kar a yi zaton za a ga yadda ake so a kasar nan.

“Idan har cigaba muke so, to dole mu rika zakulo wadanda suka fi cancanta, in kuma ba haka ba, to dakikai za mu ci gaba da dauka a matsayin jami’an tsaro.

“Dole ne mu rika daukar wadanda za su iya aikin, kuma akwai ’yan Najeriya birjik da suka cancanta,” kamar yadda ya bayyana.

– Kirkiro ’yan sanda jihohi kasada ce

Zulum ya ce kirkiro da ’yan sandan jihohi babu abin da zai yi face kara lalata sha’anin tsaro a Najeriya, saboda haka ya bukaci masu neman a kafa ’yan sandan jihohi da su zurfafa tunani kan mummunan abin da hakan zai iya haifarwa bayan tsawon lokaci.

“Tsakani da Allah, ni, Babagana Zulum, ba zan goyi bayan a yi ’yan sanda jihohi ba; Ba na so a yi, duba da irin matsalar da hakan zai haifar.

“Najeriya ba ta kai matakin yin ’yan sandan jihohi ba, wasu gwamnonin na iya amfani da su wajen kawar da kabilun da ba nasu ba.

“Saboda haka a yi hattara. Idan aka ba ’yan sandan jihohi rabin karfin ’yan sanda da sojojin Najeriya, kasar nan ta shiga uku,” inji Gwamna Zulum.