Gwamnatin Tarayya ta yi gwanjon jirgin shugaban inda take neman masu sha’awar saya su zo su taya.
Tuni gwamnati ta fitar da sanarwar neman mai sayen jirgin mai suna Falcon 900B (mai lamba NAF 961) — daya daga cikin jiragen shugaban kasa — da ke karkashin kulawar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya.
Tallar gwanjon jirgin shugaban kasar ta bukaci masu sha’awar saye su su mika takardunsu na tayin jirgin kafin ranar 24 ga watan Disamban nan da muke ciki.
A halin yanzu jirgin alfarman mai daukar fasinjoji 16 da matuka kujerun matuka uku na nan a rumfa mai lamba 307 EAG a filin Jirgi na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja domin masu son saya su je su tantance su taya.
- Kano: Lauyoyin Arewa 200 sun lashi takobin taimakon Abba a Kotun Koli
- Matashi ya yi wa makwabcinsa yankan rago saboda abinci
Sanarwar neman mai sayen jirgin wadda Air Commodore EK Gabwak, ya sanya hannu a madadin Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce, wajibi ne tayin da masu neman sayen jirgin za su yi ya kasance da Dalar Amurka.
Za kuma su iya mika bukatarsu ta intanet ko hannu da hannu ga Kwamitin Cefanar da jirgin mai mai suna Falcon 900B mai lamba NAF 961 da ke Hedikwatar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya kafin ranar 24 ga wata.