Ana zargin Hukumar Kwastam ta Najeriya da jami’anta sun karkatar da motoci 300, a yayin da take shirin yin gwanjon wasu motoci kusan 500.
Zargin na zuwa ne bayan hukumar kwastam ta sanar da fara gwanjon motoci 462 da ta kama a hannun masu laifi, wadanda darajarsu ta kai Naira miliyan 556.7.
Kakakin hukumar kwastam, Abdullahi Maiwada, ya ce tuni hukumar ta sanya hotunan motoci 476 a shafinta, domin masu sha’awa su zaba.
Kimanin mutane 14,000 ne suka tura bukatarsu ta sayen motocin ta shafin hukumar kwastam din na intanet.
- Tsadar rayuwa: Najeriya na iya fadawa cikin rikici —AfDB
- Matashi ya harbe ’yan gidansu 12 har lahira a Iran
Sai dai kuma ’yan kasuwa masu shige da ficen motoci sun yi zargin cewa hukumar da ma’aikatanta sun karkatar da wasu motoci 300.
Shugaban kungiyar dillalan motoci (NAGAFF), Alhaji Tanko Ibrahim, ya zargi hukumar da wasa da hankalin jama’a da kuma zalunci.
Alhaji Tanko ya yi zargin cewa daga cikin motocin da hukumar ta yi gwanjo su, har da wadanda masu su suke shirin biyan kudaden haraji ko na tara da aka yi musu.
A cewarsa, sanya wadannan motoci a cikin wadanda za a yi gwanjon su zalinci ne, sannan N10,000 da hukumar ta sanya a matsayin kudin rajistar masu sha’awar sayen motocin ya yi yawa.
Amma a martaninsa ta cikin wata sanarwa, kakakin hukumar kwastam, Abdullahi Maiwada, ya ce abin takaici ne yadda masu tutiyar kungiyanci suke yada labarai marasa tushe.