✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa dokar hana fita a Sabon Birni bayan tarzomar kisan Sarkin Gobir

An sanya dokar daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe sakamakon kone-konen da matasa suka yi a bisa manyan tituna, da wasu gine-gine…

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sanya dokar hana fita a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni bayan tarzomar da ta barke sakamakon kisan Sarkin Gobir Alhaji Isa Muhammad Bawa.

Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da sanya dokar daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe sakamakon zanga-zangar da kone-konen da matasa suka yi a bisa manyan tituna, da wasu gine-gine kan kisan Sarkin, wanda shi ne Hakimin Gatawa.

Kakakin rundunar, ASP Ahmed Rufa’i, ya ce dokar hana fitar za ta ci gaba da aiki har sai abin da hali ya yi.

Ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar da doka da oda da kuma hana kazancewar lamarin.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa masu zanga-zanga sun yi yunkurin koma gidajen wasu fitattun ’yan siyasa a yankin, “amma jami’an tsaro sun yi saurin zuwa suka hana su.”

Sun kuma kona Sakatariyar Jam’iyyar APC da wani dakin kotu sannan suka fasa rumbun ajiyar karamar hukumar inda suka lalata takin zamani.

Turakin Gobir, wanda dan mamacin ne ya ce an tura karin jami’an tsaro zuwa yankin.

Ya ce, “tun da safe muke jin karan harbe-harbe, amma masu zanga-zangar sun ci gaba har zuwa misalin karfe 8 a dare,” in ji shi.