✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

Dokar hana fita tsawon awa 24 a Kaduna da Zariya ta fara aiki ne nan take

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya sanya dokar hana fita tsawon awa 24 kuma ta fara iaki nan take.

Majalisar tsaron jihar ta amince da kafa wannan doka ne bayan zaman da ta yi a ranar Litinin.

Sanarwar da Kwamsihinan Tsaro na jihar, Samwel Aruwan ya fitar ta ce kwararan hujjoji sun riga sun bayyana cewa bata-gari sun shiga rigar zanga-zangar tsadar rayuwa suna fasa shaguna da saceewa da kuma lalata kayan jama’a da na gwamnati a jihar.

Aruwan ya bukaci al’ummar wuraren da dokar ta shafa da su kasance a gidajensu tare da ba wa jami’an tsaro hadin kai domin tabbtar da wannan doka.

A cewarsa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da lura da halin da ake ciki a jihar da nufin daukar mataki na gaba.

Wannan doka na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da masu zanga-zangar tsadar rayuwa suka yi arangama da jami’an tsaro a garin Kaduna.

Masu zanga-zangar, wadanda akasarinsu matasa ne da kananan yara, sun fito kan tituna ne dauke da tutar kasar Rasha.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati sun rika rera wakokin hadin kai a unguwannin da ke garin Kaduna, irin su Kawo da Unguwar Shanu da sauransu.

Sun kuma yi sa-in-sa da sojoji da ’yan sanda da suka yi kokarin shawo kansu a yayin tattakin.