A ranar Assabar da ta gabata ce, motar rushe gini mallakar Gwamnatin Jihar Sakkwato ta shiga babbar tashar mota mallakar jiha ta yi wa shagunan masu sana’a dirar mikiya, inda ta rushe su tare da lalata duk wasu kaya da ke cikin shagunan; sakamakon day a haddasa asarar dinbin kaya na miliyoyi.
Aminiya ta zanta da shugaban masu sayar da kayan mota, Alhaji Bashiru Umar a madadin sauran masu shaguna na cikin tashar gaba daya. Ya ce: “Mun yi asara mai dinbin yawa, wadda ba mu san adadinta ba. Shaguna 298 ne aka rushe mana tare da kayan da ke cikinsu da suka lalace, domin ba mu dauki komai ba daga cikin shagunan. Domin ba mu san za a zo a yi mana wannan ta’asar ba. A halin da ake ciki muna tattara hasarar kowa ne, domin sanin abin da za mu gabatar kotu a kotu.
“Fiye da mutum 2000 ne aka hana wa sana’ar da suke yi, su ciyar da kansu da iyalansu. Wani ma har danginsa da shi ne suka dogara. A wannan tashar ana sayar da kayan mota sakan da tayoyin mota da ruwaya da walda da yin wanki da guga da sayar da abinci. Wallahi da yawanmu ba mu san in da za mu dosa ba in aka tayar da mu daga nan. Mun fi shekara talatin cikin tashar nan muna sana’a, tun ba ka da wuri kana haya har ka samu kudi ka saya; yanzu a ce an rushe maka wuri wai ka tashi, gwamnati na son wurinta. Akwai adalci kuwa? Mu talakawa, mu muka zabi wannan gwamnati, in ba ta samar mana karin ci gaban sana’armu ba bai kamata ta rushe mu ba, ko don iyalanmu.” A cewar Alhaji Bashiru.
Kodineta na hukumar kula da hakkin dan Adama ta kasa, Barista Hamza Nuhu ya ce za su bi hakkin mutanen a kotu don a biya su asarar da suka yi, tare da hukunta wadanda suka bijire wa umurnin kotu, domin an yi mata laifi.
Abdullahi Bafarawa shi ne Manajan kasuwa. Ya yi magana da wakilinmu kan dalilinsu na tayar da shagunan, ya ce: “Mutanen na zaune ba tare da izini ba har sun mayar da wurin mafakar bata-gari da aikata barna. Har jarirai 4 an tsinta wurin, muka kai su gidan yara. Mun kama wani bata-garin yaro daga Nijar. Ya gaya mana cewa a tashar yake zaune. Abubuwa suna faruwa da yawa a tashar, wanda dole gwamnati ta dauki matakin tsaftace tashar da yi mata tsari mai kyau da inganci kuma mun ba su wa’adi su tashi don gyara wurin sun ki; har lokacin aikin ya zo ba wata takarda da muka samu daga kotu, cewa kar mu yi aikinmu da zai taimaki jiharmu.”