Gwamnatin Tarayya ta rusa rundunar ’yan sanda masu yaki da fashi da makami (FSARS).
Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da FSARS a ranar Lahadi.
“An soke rundunar ’yan sanda ta FSARS a dukkannin jihohin Najeriya da Birnin Tarayya inji shi”, a jawabinsa.
Ya kuma umarci dukkannin jami’an FSARS da su gaggauta gabatar da kan su a hedikwatar rundunar ’yan sanda ta kasa domin a sauya musu wuraren aiki.
Soke rundunar ta FSARS na zuwa ne bayan an shafe kwanaki ana zanga-zangar neman hakan a sassan Najeriya bisa zargin jami’anta da cin zalin jama’a.
Shugabbani da mafutika da matasa sun yi ta Allahwadai da yadda jami’an ke zaluntar jama’a, lamarin da ya sa Shugaban Kasa cewa zai gyara wa rundunar zama.
Buhari ya kuma umarci Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da ya kama tare da hukunta jami’an da zargi ya tabbata a kansu domin yin maganin ’yan sandan da ke daukar doka a hannunsu.
Ko da yake wasu ’yan Najeriya na ganin gyaran fuska ya kamata a yi wa rundunar, wasu na ganin hakan ba zai biya bukata ba domin a baya ma an yi irin wadannan koke-koke a kan jami’an, wanda sakamakonsa ne aka sauya wa rundunar suna daga SARS.
Akwai kuma masu ganin cewa sokewar ba za ta kawo wani sauyi ba domin jami’an da ake zargin za su ci gaba da aikin dan sanda a kasar da ake yawan zargin jami’an ’yan sanda da karbar na goro da kuma amfani da kakinsu wajen danne hakkin jama’a.
Don haka suke ganin abin da ya fi dacewa shi ne wayar da kan jami’an ’yan sanda ta yadda za su fahimci muhimmancin aikinsu da kuma gudanar da shi cikin kare hakkin jama’a.