Gwamnatin Jihar Adamawa ta rufe daukacin makaratun da ke jihar a dukkanin matakai nan domin takaita yaduwar cutar COVID-19.
Ta bayar da umarnin bayan Gwamantin Tarayya ta umarci a ci gaba da kiyaye matakan kariyar COVID-19 wadda ta ke kara bazuwa a karo na biyu a Najerya.
- Daliban Kankara sun sauka a Gidan Gwamnatin Katsina
- Yadda muka sasanta aka sako Daliban Kankara ba biyan kudin fansa
Babbar Sakatare a Ma’aikatar Ilimi da Inganta Rayuwa, Aishatu Abubakar ta ce: “Ma’aikatar na umartar a rufe dukkannin makarantu nan take daga ranar 17 ga Disamba, 2020.
“Za a sanar da ranar budewa nan gaba, saboda haka shugabannin dukkanin makarantu su kiyaye.”
Sanarwar na zuwa ne kwana guda bayan jihar Kaduna ta dauki makancin matakin bayan yaduwar cutar a jihar.
Jihar Kano ma ta rufe dukkannin makarantu duk da cewa ba ta bayyana dalilin daukar matakin ba.
Sai dai jihar na daga cikin wadanda a baya-bayan nan suka nuna damuwarsu game da karuwar masu kamuwa da cutar ta COVID-19.