Gwamnatin Tarayya ta ce matsalar ’yan bindiga a Jihar Neja ta tilasta rufe makarantu kimanin 400 a sassan Jihar.
Ministar Tallafi da Ayyukan Jinkai, Beta Edu ta bayyana cewa a sakamakon haka, kananan yara sama da 11,00 ne suka daina zuwa makranta a yankunan jihar da ke fama da matsalar tsaro.
- Tinubu ya dawo da tallafin mai; ya biya N169bn a Agusta
- An cafke kwandasta kan zargin fyade a cikin mota
Da take kaddamar da rabon kayan tallafi ga ’yan gudun hijira da ’yan bindiga suka raba da gidajensu a yankin Gwade na Karamar Hukumar Shiroro ta jihar, Ministar ta nuna damuwarta bisa yawan yaran da suke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba, duk da cewa ilimi shi ne ginshikin kawar da miyagun dabi’u da kuma samar da abin dogaro da kai a al’umma.
“Mun zo ne mu ga halin da ake ciki domin sanin matakin da za mu dauka, kuma mun fara tunanin samar wa masu gudun hijira matsuguni.
“Samu samar da wurin da za a tsugunar da su su ci gaba da rayuwa saboda ’ya’yanku su rika samun zuwa makaranta.”
A cewarta, gwamnati na shirin fadada rajistar masu bukatar tallafi domin sanya ’yan gudun hijira a jerin masu cin gajiyar tsare-tsarenta na tallafi.
Kwamishinan tallafi da ayyukan jinkai na Jihar Neja, Ahmed Suleiman, ya ce a halin yanzu mutum 22,071 ke gudun hijira a sakamakon ayyukan ’yan ta’adda da suka addabi 11 daga cikin kananan hukumomi 25 na jihar.
Ya ce a sakamakon haka, makarantun firamare da sakandare na da gaba da su da suka koma matsugunin wucin gadi na ’yan gudun hijira, sun yi kadan, duk da cewa hakan ya hana su samun ilimi.
“’Yan gudun hijira a sansanonin da ke kananan hukumomin Kontagora, Mariga, Mashegu, Rijau, Rafi, Mokwa da Munya ba su da matsuguni da sauran abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha, magani, makarantu, da makewayi,” a sakamakon rashin tsaro.