✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe makarantar da ake zargin malamai sun kashe dalibi da duka a Zariya

Malaman sun zane yaron ne bayan ya daina zuwa makaranta na wasu kwanaki.

Hukumar Kula Da Ingancin Makarantu ta Jihar Kaduna ta rufe makarantar Al-Azhar da ke Zariya kan zargin kashe wani dalibi da duka.

A ranar Asabar ne aka bayar da rahoton mutuwar wani dalibi dan aji uku a sakandare wanda ya rasu kan zargin duka mai tsanani da wasu malamai suka yi masa har suka cire masa hakora.

Rahotanni sun ce malaman sun zane yaron ne bayan ya daina zuwa makaranta na wasu kwanaki sakamakon an bukaci ya maimaita aji bayan ya fadi jarabawar zuwa aji na gaba.

Cikin wata sanarwa da darakta janar na hukumar ta KSSQAA, Dakta Usman Abubakar ya fitar a ranar Lahadi, ta ce Ma’aikatar Ilimi karkashin wakilcin gwamnatin jihar ta kaddamar da bincike kan lamarin.

Ya bayyana cewa sun kai ziyara zuwa Zariya domin tattara bayanai kan hakikanin abin da ya faru a makarantar Al-Azhar Academy wanda a nan lamarin ya faru da gidan su mamacin domin yin ta’aziyya ga iyalansa da wasu abokan karatunsa.

Haka kuma Abubakar ya bayyana cewa sun kai ziyara hedikwatar ‘yan sanda a Zariya wanda a nan ne shugaban makarantar da mataimakinsa ke tsare.

Haka kuma shugaban hukumar ta KSSQAA ya ce sun kai ziyara makabartar da aka binne yaron.

Ya kuma bayyana cewa makarantar ta Al-Azhar za ta ci gaba da zama a rufe har sai abin da bincike ya nuna.

Sanarwar ta kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankulansu, tare da bin doka da oda, yayin da ta ce ma’aikatar ilimin jihar na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Matashiya

Aminiya ta ziyarci gidan iyayen dalibin da ya rasu, wato gidan Alhaji Sambo da ke unguwar Kofar Kuyanbana cikin birnin Zariya.

Isa Sa’idu, daya ne daga cikin iyalan da ya bayyana mana yadda lamarin ya faru inda ya ce, “A jiya da safe abokin mahaifin marigayi ya dauke shi zuwa makarantar sakamakon marigayin ya daina zuwa, wai saboda an koma da shi ajin baya don haka ya ce baya son makarantar.

“Wanda ake zargi da aikata kisan ya ce ya damka marigayin a hannun Mataimakin Shugaban makaratan, kuma ya ce tun a gabanshi ya fara dukan marigayin.”

‘An yi masa bulala sama da 100’

Malam Isa, ya kara da cewa a bayanin da suka samu daga abokan karatun dalibin a makarantar shi ne an gabatar da shi a gaban daliban aka yi masa bulala kusan 100, daga nan kuma aka kai shi ofishin Shugaban Makaratan, inda a nan ma aka sake tube masa riga aka ci gaba da dukan shi har sai da wasu daga cikin hakoransa suka fice daga bakinsa.

Daga nan da suka ji ba ya numfashi sai suka kai shi hanyar suka shimfidar da shi, sannan suka kai shi asibiti.

Bayanan da Aminiya ta samu na nuni da cewa duk da mutuwar wannan dalibi, mahukuntar makarantar ba su sanar da iyayensa ba har sai da iyayen yaron suka rika jin rade-radin cewa an kai shi asibitin Al-Ridha Clinic da ke kusa da makarantar.

“A nan ne suka garzaya asibitin domin su tabbatar da gaskiyar labarin. Da isar su asibitin sai likitan da ya duba yaron ya tabbatar musu da cewa shi ne ya duba yaron, kuma gawa aka kawo musu, ba mara lafiya ba,” in ji Isa.

Da wakilinmu ya ziyarci makarantar domin tabbatar da gaskiyar lamarin, ya tarar da makarantar a kulle saboda yau [Asabar].

Sai dai mun zanta da wasu daga cikin daliban makarantar da suka kai ziyarar ta’aziyya gidan abokin karatun marigayin.

Daya daga cikin yaran wanda suke aji daya da dalibin kuma muka sakaya sunansa, ya ce, “Mataimakin Shugaban Makarantar shi ya zo da yaron gaban “assembly” inda suka rika yi masa bulala babu kakkautawa tare da Shugaban Makarantar, tun muna iya kirga bulalar har muka bata lissafi, ko ni na kirga bulala akalla 105 wanda aka yi wa marigayin a gabanmu,” in ji dalibin.

“Daga nan kuma suka wuce da shi zuwa ofishin Shugaban makarantar, suka cire masa riga, suka bar shi da gajeren wando kawai suka ci gaba da dukansa har yaron ya yi yunkurin guduwa, amma aka sa shuwagabannin daliban makarantar suka rike shi suka koma da shi, aka ci gaba da dukansa har sai da suka cire masa hakora, suka kashe shi,” in ji shi.

‘A kan rashin zuwa makaranta aka yi masa hukuncin’

Aminiya ta gano cewa ana zargin an yi wa dalibin hukuncin ne saboda dalibin ba ya son zuwa makaranta kullum saboda kunya da yake ji na komawa da shi ajin baya da aka yi smasa akamakon rashin yin kokari a aji.

“Bayan sun kashe Marwanu sai suka fito da gawar waje, suka ajiye shi a hanyar zuwa bandaki har aka tashi makaranta,” in ji dalibin.

Sai dai har zuwa lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan mahukuntan makarantar ba su ziyarci iyalan mamacin ba domin jajanta musu.