✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe shugabar majami’ar Yahudawa a Amurka

An yi wa Babbar Limamiyar Yahudawa kisan gilla a kasar Amurka inda jami'an tsaro suka tsinci gawarta a caccaka mata wuka

An yi wa shugabar wurin ibadar Yahudawa kisan gilla a kasar Amurka inda jami’an tsaro suka tsinci gawarta a caccaka mata wuka.

A ranar Asabar ’yan sanda suka tsinci gawar Samantha Woll mai shekaru 40 da sara a wurare daban-daban a jikinta, a gidanta da ke yankin Detroit.

Babban jami’in ’yan sanda na yankin, James White, ya ce jinin da suka gani ne ya kai su gidanta, inda suka tsince ta kwance cikin jini a harabar gidan.

Ya ce ba a kai ga gano dalilin kisan ba, kuma ya bukaci jama’a da su guji hasashen wanda ya aikiata, su jira a kammala bincike kisan shugabar majami’ar Yahudawan.

Gisan gillan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da wa juna kallon hadarin kaji tsakanin al’ummar Musulmi da Yahudawa a sakamakon rikin Falasdinawa da Isra’ila da ya yi ajalin mutane kusan bakwai tare da jikkata wasu kimanin dubu 14.

Kimanin mako guda ke nan da wani tsoho mai shekaru 71 magoyin bayan Yahudawa ya yi wani karamin yaro dan shekara shida kisan gilla ta hanyar caka masa wuka sau 26 a Amurka.

Samantha Woll hadima ce ga ’yar majalisar wakilan Amurka Elissa Slotkin ta Jam’iyyar Demokrat.Slotkin, ta bayyana cewa Woll na daga cikin masu fafutikar “samar da fahimta tsakanin addinai,” musamma Musulmi da Yahudawa.

’Yar Majalisar AMukar, Rashida Talaib, ta bayyana kaduwa da kisan gilla da aka yi marigayiya Woll wadda ta ce “abokiyarta” ce.