Majalisar Dokokin Jihar Binuwai ta dakatar da ayyukanta bayan shugabanta, Titus Uba da wani daga cikin ’ya’yanta sun kamu da cutar coronavirus.
Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kai na Majalisar Tertsea Gbishe a cikin wata sanarwar a safiyar Litinin ya ce Majalisar na jiran sakamakon gwajin da aka yi wa ragowar ’ya’yanta.
“Zuwa yanzu jami’an hukumar NCDC [mai yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya] sun tabbatar da kamuwar Rt. Hon. Titus Uba da Hon. Tertsea Gbiseh da cutar, yayin da ake jiran sakamakon ragowar ’Yan Majalisar.
“Saboda haka Shugaban Majalisar ya umarci a rufe ta nan take a kuma yi feshin magani”, inji Tertsea wanda shi ma ke dauke da cuta.
Ya kara da cewa tuni wadanda suka kamu da cutar suka killace kansu ana duba lafiyarsu bisa tsarin jinyar masu ita, duk da cewa babu alamar ta a tare da su a zahiri.
“A halin yanzu za a rikan sanar da ‘yan majalisa duk wani muhimmin abin da ya ya kamata ta tsarin taron zamani (videoconferencing)”, inji sanarwar.