Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba da umarnin rufe Kwalejin Nuhu Bamalli da ke garin Zariya a jihar, biyo bayan sace wasu dalibai da malamai da wasu ’yan bindiga suka yi a ranar Alhamis.
Har ya zuwa yanzu ba a san adadin mutanen da ’yan bindigar suka sace a Kwalejin ba.
- Zamfara: An dakatar da Sarkin Zurmi kan ayyukan ’yan bindiga
- Buhari ya mika karin kasafin biliyan N895 ga Majalisa
Kai hari makarantu tare da sace dalibai da malamai ba sabon abu bane a Jihar Kaduna, inda a cikin shekarar nan ’yan bindiga sun yi garkuwa da daliban Kwalejin Gandun Daji da ke Afaka da kuma dalibai da ma’aikatan Jami’ar Greenfield duk a jihar ta Kaduna.
Matsalar garkuwa da mutane na ci gaba da kamari a yankin Arewa maso yammancin Najeriya, musamman a Jihohin Kaduna, Katsina, Sakkwato, Zamfara da Kebbi.
Ita ma Jihar Neja na fama da matsalar masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga da ke ci gaba da kai hare-hare.
A baya-bayan nan ma sai da wasu ’yan bindiga suka sace daliban Islamiyya a garin Tegina da ke jihar, wanda adadinsu ya haura 100.