✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe Jami’ar KASU kan karin kudin makaranta

A karshe an rufe jami'ar saboda zanga-zangar dalibai kan karin kudin makaranta.

Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta rufe harkokin karatun dalibai da ke matakin digirin farko saboda zanga-zangar daliban kan karin kudin makarantar.

Rajistaran Jami’ar KASU, Samuel S. Manshop ya sanar cewar rufewar za ta ci gaba daga ranar Talata har sai abin da hali ya yi; Ranar Talatar ce daliban suka yi zanga-zanga a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna don neman a janye karin kudin makarantar.

Aminanshi sun kashe shi kan bashin da yake bin su

“Hukumar Gudanarwar Jami’ar KASU na sanar da ma’aikata, dalibai da daukacin al’umma cewa ta dakatar da harkokin karatun daliban digirin farko sai abin da hali ya yi.

“Amma daliban gaba da digirin farko da masu karatu a bangaren aikin likita da bangaren hada magunguna da masu karatu-lokaci-zuwa-lokaci za su ci gaba da daukar darussa,” inji sanarwar da ya fitar.

Sai dai sanarwar ta umarci daukacin ma’aikata su ci gaba da zuwa wurin aiki, kafin a sanar da su abu na gaba.

Rufewar na zuwa ne bayan shafe makonni daliban Jami’ar KASU suna  gudanar da zanga-zanga tun bayan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi karin kudin.

Tun lokacin da ake rade-radin karin kudin iyaye da dalibai suke yin tir da shi, kafin daga baya Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta ce karin bai kai yadda ake cewa ba.

A halin yanzu dai an ninka kudin makarantar jami’ar akalla sau hudu, kuma tun lokacin dalibai ke ta gudanar da zanga-zangar neman a janye.

Amma kuma, Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce babu makawa a karin kudin, wanda ta ce ta yi ne da nufin inganta karatun jami’a.