Kwamitin yaki da annobar COVID-19 a Birnin Tarayya ya rufe cibiyoyin killace masu cutar guda uku bayan raguwar masu kamuwa da ita.
Yanzu haka a Abuja cibiyoyin killace masu dauke da cutar hudu ne ke aiki.
- Tsohuwa mai shekara 100 ta warke daga coronavirus
- Har yanzu annobar coronavirus ba ta gushe ba –Sule
- Coronavirus ta kashe Sanata Buruji Kashamu
- Ministan da ya kamu da coronavirus ya koma aiki
Shugaban kwamitin, Ejike Oji, ya ce “Yanzu haka mun rufe cibiyar killace masu cutar da ke babban asibitin Asokoro, Babban Asibitin Karu da kuma Cibiyar Idu da take da gadaje 500”.
“Cibiyoyin da suke aiki a yanzu su ne Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, Asibitin Tarayya na Gwagwalada, Cibiyar ‘ThisDay’ da kuma otal guda daya”.
Ya kara da cewa sun dauki matakin rufe cibiyoyin ne ganin yadda aka samu raguwar samun masu dauke da cutar.
Ya bayyana fatan kada a sake samun dawowar cutar a karo na biyu kamar yadda wasu kasashen Turai ke fuskanta.
Da aka masa tambaya game da abin da cakuduwar jama’a a lokacin zanga-zangar #EndSARS ka iya haifarwa, jami’in ya ce a yanzu dai babu wasu alkaluma da suka nuna an sake samun masu cutar duk da cewar mutane sun karya dokokin da aka shimfida na kariya.