An rufe Babban Masallacin Juma’a na Agege da ke Legas bayan da wasu masallata suka jefi jami’an Kwamitin Cika-Aiki na Gwamnatin Jihar Legas kan Hana Yaduwar Coronavirus.
Masarautar Agegen ce dai ta dauki matakin bayan mahukunta a jihar ta Legas sun fitar da wata sanarwa cewa masallatan sun kai wa jami’ansu hari a lokacin sallar Isha’i.
A sanarwar, shugabar kwamitin, Dokta Dolapo Fasawa, ta ce masallata sama da 300 ne suka taru don yin sallar, lamarin da ya sa jami’an tsayawa domin su yi masu nasiha, amma bayan idar da sallar sai wasu mutane daga cikinsu suka fara yi masu sowa, suna kabbara suna jifansu da duwatsu har sai da jami’an tsaro suka kai masu dauki.
Masallacin da lamarin ya auku wanda aka fi sani da Masallacin Alaja da ke unguwar Zango a Agege daya ne daga cikin manyyan masallatan juma’a a Legas.
Mai Unguwar Zango Alhaji Auwal Muhammad ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne dai a lokacin sallar Magariba.
“Jami’an Kwamitin Cika-Aiki na Gwamnatin Legas mai yaki da yaduwar coronavirus sun zo wucewa sai suka fuskanci akwai taron jama’a a masallacin suna sallar Magariba, sai suka tsaya.
“Bayan an idar suka nemi su yi wa jama’a jawabi a hukumance game bukatar kiyaye dokokin hana yaduwar cutar; sun fara bayanin cikin ruwan sanyi sai aka sami wasu bata-gari, zauna gari banza suka fara masu ihu da sowa, suna jifansu.
“Wannan abu bai mana dadi ba, kuma tuni Masarautar Agege ta rufe masallacin, yanzu babu kowa a ciki, an hana jama’a zama a harabarsa, an kuma bai wa masu sayar da kayayyaki a harabar masallacin umarnin su rufe kayansu su bar wajen”, inji Alhaji Auwal.
Haka zalika Magatakardan Masarautar Agege Alhaji Abubakar Aliyu Na’ibi ya shaida wa Aminiya cewa masarautar ta yi tir da lamarin, yana cewa tun bayan da gwamnatin Legas ta kafa dokar hana taro a wuraren ibada masarautar ta ba da umarnin rufe masallatai da ka iya tara jama’a fiye da kima.
“Tun a ranar da lamarin ya faru Mai Martaba Sarkin Agege Alhaji Musa Dogonkadai ya ba da umarnin rufe masallacin baki daya, yanzu haka masallacin na rufe ba a yin ko wacce sallah a ciki”, inji shi.
Masallacin Juma’a na Alaja da ke unguwar Zango a Agege masallaci ne da ke tara dimbin jama’a a lokutan sallar Juma’a da kuma salolli biyar, kasancewarsa a tsakiyar garin Agege, a kuma cikin kasuwa, sannan a unguwar Zango inda nan ne tushen ‘yan arewa mazauna Legas.