✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rufe asibiti saboda jinyar masu COVID-19 ‘mai tsanani’ a Kano

Ana zargin asibitin da kwantar da masu fama da COVID-19 mai tsanani

Gwamnatin Jihar Kano ta garkame wani asibiti da ke birnin Kano saboda zargin sa da jinyar masu cutar COVID-19 mai tsanani.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ya ce an rufe asibinin UMC ne saboda hukumar gudanarwarsa ya bari ana jinyar da masu COVID-19 mai tsanani, sabanin cibiyoyin killace masu cutar da gwamnatin jihar ta tanadar.

Ya ce hakan ya saba da ka’iadar da Kwamitin Yaki da COVID-19 a Jihar ta sanya wanda ya takaita asibitoci ga kula da cutar a matakin da bai yi tsanani ba.

Ya ce sakacin ya yi sanadiyyar rasuwar mutum biyu masu cutar: daya a asibitin, daya kuma a hanyar zuwa asibitin.

Malam Garba, who was in company with the commissioner for health,

A lokacin ziyarar da Kwamishinan Lafiyan Jihar, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya kai asibitin da aka rufe, Muhammad Garba ya ce asibitin zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an daidaita tsakanin hukumar gudanarwar asibitin da Gwamnatin Jihar.

Ya ce an mayar da mutum biyu masu cutar mai tsanani da ke asibitin zuwa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano,

Sauran marasa lafiya kuma an mayar da su Asibitin Kwararru na Muhammadu Abdullahi Wase da ke unguwar Nasarawa.