✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da sabon shugaban mulkin soja na Burkina Faso

A ranar 30 ga Satumba Traore ya jagoranci sojoji suka tuntsurar da gwamnatin Damiba, mai wata takwas kacal a mulki.

An rantsar da Ibrahim Traore wanda ya jagoranci juyin mulkin kasar Burkina Faso a matsayin sabon shugaban kasa.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a babban binin kasar, Ougadouou a inda a ka tsaurara matakan tsaro a ranar Juma’a.

Sabon shugaban ya ayyana mulkinsa a matsayin na rikon kwarya, wanda a cewarsa, zai mika mulki ga farar hula bayan gudanar da zabe a watan Yulin shakarar 2024.

A jawabinsa bayan rantsuwar, Traore na mai cewa, kasar tana cikin babbar barazana ta dorewa, a inda take fama da matsalolin tsaro da na jinkai, wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar.

“Manufarmu ita ce mu kwato yankunan kasarmu da ke hannun ’yan ta’adda,” in ji sabon shugaban mulkin sojan.

A ranar 30 ga watan Satumba ne Traore ya jagoranci wasu fusatattun sojoji, a inda  suka tuntsurar da gwamnatin Damiba, mai wata takwas kacal a mulki.

Wanda aka yi wa juyin mulkin Damiba, shi ma kwatar mulkin ya yi daga shugaban da aka zaba, Roch Marc Christian Kabore a watan Janairun shekarar 2022.