An rantsar da Ibrahim Traore wanda ya jagoranci juyin mulkin kasar Burkina Faso a matsayin sabon shugaban kasa.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a babban binin kasar, Ougadouou a inda a ka tsaurara matakan tsaro a ranar Juma’a.
Sabon shugaban ya ayyana mulkinsa a matsayin na rikon kwarya, wanda a cewarsa, zai mika mulki ga farar hula bayan gudanar da zabe a watan Yulin shakarar 2024.
A jawabinsa bayan rantsuwar, Traore na mai cewa, kasar tana cikin babbar barazana ta dorewa, a inda take fama da matsalolin tsaro da na jinkai, wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar.
“Manufarmu ita ce mu kwato yankunan kasarmu da ke hannun ’yan ta’adda,” in ji sabon shugaban mulkin sojan.
A ranar 30 ga watan Satumba ne Traore ya jagoranci wasu fusatattun sojoji, a inda suka tuntsurar da gwamnatin Damiba, mai wata takwas kacal a mulki.
Wanda aka yi wa juyin mulkin Damiba, shi ma kwatar mulkin ya yi daga shugaban da aka zaba, Roch Marc Christian Kabore a watan Janairun shekarar 2022.