✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da Mahamat Deby a matsayin Shugaban Chadi

Deby ya ce ya rantse "a gaban al'ummar Chadi… don yin ayyukan al'ummar ƙasar.

A ranar Alhamis ne aka rantsar da Janar Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya jagoranci mulkin sojan Chadi na tsawon shekaru uku, a matsayin shugaban kasa.

Deby a hukumance ya lashe kashi 61 cikin 100 na kuri’un da aka kada a ranar 6 ga watan Mayu wanda kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa suka ce ba a yi adalci ba.

Da yake karɓar rantsuwa, Deby ya ce ya rantse “a gaban al’ummar Chadi… don cika manyan ayyukan da al’ummar ƙasar ta ɗora mana”.

Shugabannin Ƙasashen Afirka takwas da kuma mambobin majalisar tsarin mulkin kasar da ɗaruruwan baƙi sun halarci rantsar da matashin mai shekaru 40.

Mahamat Deby dai ya doke abokin babban hamayyarsa, Firayim Minista Succes Masra, wanda ya samu kashi 18.5 cikin 100.

A cikin 2021, Deby ya samu amincewa cikin gaggawa daga kasashen duniya karkashin jagorancin Faransa, wadanda gwamnatocin sojoji suka kori dakarunta a shekarun baya a sauran kasashen da suka yi wa mulkin mallaka na Mali, Burkina Faso da Nijar.

Firai Minista Succes Masra, daya daga cikin masu adawa da Deby kafin ya zama firaminista, ya mika takardar murabus dinsa a ranar Larabar da ta gabata, sakamakon shan kaye da jam’iyyarsa ta yi a zaben bayan watanni hudu.