Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya rantsar da Mai Shari’a Dije Audu Aboki a matsayin mace ta farko da ta zama Alkaliyar Alkalai ta jihar.
Bikin nadin ya gudana ne a dakin taro na Africa House da ke Fadar Gwamnatin Kano a ranar Litinin.
- ECOWAS za ta yi sabon taro kan juyin mulkin soji a Nijar
- Makarantu 79 na da malami 1 kowannensu a Bauchi
Gwamnan ya bukaci bangaren shari’a da su mara wa kokarin gwamnatinsa baya na rushe gine-gine da kuma kwato kadarorin al’umma da ake zargin gwamnatin baya ta yi ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin bangarorin gwamnatin uku.
“Dangantakar da ke tsakanin bangaren shari’a, majalisa, da zartarwa ba gasa ba ce,” in ji shi.
Ya bayyana kudurinsa na ci gaba da kyautata alaka a tsakanin wadannan rassa.
Gwamnan ya yaba da sadaukarwar da Mai Shari’a Aboki ta yi a fannin shari’a, inda ya ce, “Mai shari’a Aboki ta biya hakkokinta na shari’a bisa kwarewa, hazaka, da kishin kasa cikin ikonsa Allah Ya daukaka matsayinta zuwa babban alkalin jihar.”
Abba ya bayyana bukatar gaggauta magance miyagun laifuka, inda ya ce, “A ra’ayinmu idan aka gaggauta aiwatar da irin wadannan shari’o’in kuma aka hukunta wadanda aka samu da laifi, hakan zai hana wasu aikata laifuka.”
A nata martanin, Mai shari’a Aboki ta nuna jin dadinta da samun damar yin aiki tare da yin alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci a aikinta.
Ta bayyana aniyarta na dawo da martabar shari’a a Jihar Kano tare da yin kira da a ba ta goyon baya da hadin kai daga bangaren zartarwa, ‘yan majalisu da na shari’a, da kuma hukumomi a jihar.
Sabuwar Atoni-Janar din ta yi alkawarin dawo da martabar bangaren shari’a.
A yayin kaddamar da Mai Shari’a Aboki a Jihar Kano, ta dauki wani muhimmin mataki na inganta bambancin jinsi da karfafa tsarin doka a jihar.