✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rantsar da Ademola Adeleke a matsayin Gwamnan Osun

Ya ce zai gyara abin da ya kira rashin adalcin gwamnatocin baya.

An rantsar da Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a hukumance a matsayin sabon gwamnan Jihar Osun.

Babban Alkalin Alkalan Jihar, Mai Shari’a Adepele Ojo ne ya rantsar da sabon gwamnan tare da mataimakinsa a filin wasa na Osogbo, babban birnin jihar.

Yayin da yake jawabi bayan shan rantsuwar kama aikin, Mista Adeleke ya ce zai gyara abin da ya kira “’rashin adalci” da cin hanci ko wasu tsare-tsare da gwamnatocin da suka gabata suka aikata wa al’ummar jihar.

Ya kara da cewa “Ina so in fada cewa tun daga fannin ilimi da lafiya da bangaren ma’adinai, da fannin noma da tituna da ruwan sha ba za su kara zama matsalolin jiharmu ba kamar yadda suke a baya.”

A watan Yuli ne Mista Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar, inda ya yi nasara a kan abokin hamayyarsa, gwamna mai ci Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC.