Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance wasu sabbin kwamishinoni huɗu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi amincewarta.
Daga cikin waɗanda majalisar ta tantance a wannan Talatar har da Mustapha Rabiu Musa, ɗan tsohon Gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
- Tinubu ya halarci bikin rantsar da shugaba mafi ƙarancin shekaru a Afirka
- An tsinci gawar Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Oyo
Sauran waɗanda majalisar ta tabbatar wa naɗin sun haɗa da Adamu Aliyu Kibiya, Abduljabbar Umar Garko da Shehu Usman Aliyu.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar sunayen kwamishinonin huɗu da ya naɗa domin tantancewa.
Bayanai sun ce majalisar ta tabbatar da naɗin dukkanin kwamishinoni ba tare wata jayayya ba, inda aka riƙa yi musu umarnin su duƙar da kai da ke nuna alamar girmamawa ga ’yan majalisar da suka amince da naɗin.
Dan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Doguwa, Alhaji Salisu Ibrahim Riruwai, ya ce sun amince da naɗin sabbin kwamishinonin bayan sun tabbatar da cancantar kowannensu musamman a fannin kawo ci gaba ga Jihar Kano.
Da yake jawabi bayan an kammala tantance kwamishinonin, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawal Hussaini Dala, ya ce daga cikin ka’idar tantancewar ita ce mutum ya kasance ɗan Nijeriya kuma wanda bai gaza shekaru 30 ba sannan kuma ba a taba kama shi da wani mugun laifi ba.
Naɗin sabbin kwamishinonin na zuwa ne bayan da Gwamnan Kano ya miƙa wa majalisar buƙatar kafa wasu sabbin ma’aikatu huɗu da suka haɗa da ma’aikatar jin-ƙai, makamashi, albarkatun ƙasa da tsaron cikin gida.