✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An raba wa ’yan gudun hijira sabbin gidaje 580 a Borno

Tuni 'yan gudun hijira 4, 967 a jihar suka dace da kyautar gidaje da gwamnatin jihar.

Gwamnatin Jihar Borno ta gwangwanje ’yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita da sabbin gidaje masu daki biyu guda 580.

An gina gidajen da aka raba ne dai a yankin Auno da ke Karamar Hukumar Konduga ta jihar.

  1. Zan ba wa masu tada tarzoma a Najeriya mamaki — Buhari
  2. Matsalar tsaro: Buhari ya gana da shugabannin INEC

Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, wanda ya jagorancin bikin bude gidajen a ranar Laraba ya ce wannan na daga cikin shirin Gwamnatin Jihar na rage cunkuso a sansanonin ’yan gudun hijira a fadin jihar.

Gwamnan dai ya raba takardar shaidar mallakar gidajen ga wadanda suka amfana, tare da horon kwamitin kula da rabon gidajen kan ya tabbatar mutanen sun koma gidajen nasu cikin kankanin lokaci.

Zulum ya ce Gwamnatin ta yi alkawarin fito da nagartattun tsare-tsare wajen rufe ilahirin sansanonin ’yan gudun hijirar da ke fadin jihar tare da sama musu matsugunai.

Gwamnan ya kuma ce da yawa daga cikin mazauna sansanonin ’yan gudun hijirar na wucin gadi na fama da matsalolin karuwanci, sha da fataucin miyagun kwayoyi da cin zarafi daga ma’aikatan kungiyoyi masu zaman kansu.

Tuni dai Gwamnatin Jihar ta ba da umarnin rufe sansanin ’yan gudun hijara na wucin gadi da ke Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci ta Mohammed goni da kuma sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC), wanda a nan wasu ’yan gudun hijira ke zaune.

Ma’aikatar Gidaje da Sauya Fasalin Muhalli ta jihar ce ta gina gidajen, karkashin gudanarwar shugaban kwamitin, Injiniya Mustapha Gubio da hadin gwiwar mai bai bada shawara ta musamman ga ma’aikatar jin kai da tallafawa jama’a, Dokta Mairo Mandara.

Da yake nasa jawabin, Injiniya Gubio, ya bayyana cewa mutum 4, 967 sun samu kyautar gidaje a yankunan Damasak da Auno da Bama da Konduga da Jere da Maiduguri da kuma Marte.

Ya kara da cewa an raba gidajen ne ga malaman makarantun Firamare, malaman asibiti da jami’an tsaro.

Kazalika, ya ce nan ba da jimawa ba, Gwamnatin Jihar za ta sake kaddamar da rabon wasu sabbin gidajen a Kaleri da Warabe da Chibok da Ngarnam da Damboa da Marte da Dalori da ma wasu yankunan da dama.

%d bloggers like this: