✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An raba gardama kan mallakar Masallacin Juma’a a tsakanin ’yan darika da ’yan Izala

karamar Hukumar Potiskum da hadin gwiwar Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci ta Jihar Yobe sun kawo karshen takaddamar da ke shirin tasowa a tsakanin…

karamar Hukumar Potiskum da hadin gwiwar Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci ta Jihar Yobe sun kawo karshen takaddamar da ke shirin tasowa a tsakanin ’ya’yan kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah da ’yan darika dangane da fafutikar da suke yi na mallakar wani masallaci a Korama da wani attajiri Alhaji Umaru Kwalla ya gina a kan hanyar Maiduguri zuwa Jos daura da Unguwar Gishuwa Dabuwa a cikin garin Potiskum.
Aminiya ta samu bayanin da ke cewa takaddamar ta taso ne a tsakanin ’yan Izala da ’yan darikar  a sakamakon neman mallakar masallacin tun kafin a kammala aikinsa da aka dauki shekaru ana yi.
Ganin cewa lamarin zai haifar da rikici ne sai sabon shugaban kwamitin riko na karamar Hukumar Potiskum Alhaji Muhammad Musa Potiskum da Kwamishinan Ma’aiktar Kula da Harkokin Addini ta Jihar Alhaji Mala Musty suka yi hobbasar da ta kai ga nasarar shawo kan lamarin tare da kawo karshen takaddama ta hanyar sulhu tare da mika masallacin ga ’yan darika yayin da su kuma ’yan Izala da suka nuna halin hakuri aka umarci su nemi wani fili a garin Potiskum za a saya musu tare da yiwuwar gwamnati ta gina musu wani masallacin kwatankwacin masallacin na Korama.
Da Aminiya ta tuntubi shugaban karamar hukumar a kan ka’idojin aka bi don cimma nasarar wannan sulhu, ya ce gani aka yi kada a samu matsala dangane da rashin fahimta idan aka ce ’yan Izala ne za su rika gudanar da Sallar Juma’a a masallaci na Korama saboda daura da shi akwai masallacin ’yan darika da ake gudanar da Sallar Juma’a. Ya ce hakan aka duba aka ba da hakuri ga ’yan Izala suka kuma amince da hakan.
Shugaban ya kara da cewa, sun kafa kwamitin mutum bakwai da za su taimaka don samo filin da ya dace wanda gwamnati za ta saya wa ’yan Izala a cikin garin Potiskum don gina masallacinsu makwafin wancan na Korama wadda akwai yiwuwar gwamnati ta dafa musu don gina masalllacin in gwamnatin ta shawarta a kan haka domin samar da maslaha.