Majalisar Wakilan Najeriya ta lashi takobin kulla alaka da masu ruwa da tsaki don ganin an kubutar da daliban makarantun gaba da sakandire da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.
Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya gudana a ranar Talata.
- Gobara ta lakume rayukan mutum 12 da dukiyar Naira miliyan 17 a Kano
- An kara sako dalibin Jami’ar Greenfield
Wannan na zuwa ne yayin da Iyayen daliban kwalejin harkokin noma da gandun daji ta Kaduna suka gudanar da zanga-zanga a harabar ginin majalisa a Abuja, domin neman a ceto ’ya’yansu da ’yan bindiga suka sace a watan Maris.
Aminiya ta ruwaito cewa, Iyayen dalibai 39 da aka sace a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka aJihar Kaduna, sun yi zanga-zanga a Abuja don neman a kubutar da ragowar daliban 29 da suka rage a hannun ’yan bindiga.
Sun yi zanga-zangar ne tare da kungiyar daliban kwaleijin, kwanaki kadan bayan ’yan bindiga sun yi barazanar kashe ragowar daliban da suka sace daga Jami’ar Greenfield da ke Jihar, idan ba a biya kudin fansa ba.
Ana iya tuna cewa, a ranar 20, ga watan Maris ne wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da daliban a kauyen Kasarami na Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Haka kuma, wasu ’yan bindigar sun yi garkuwa da dalibai 22 a Jami’ar Greenfield, inda daga bisani suka kashe biyar daga cikinsu domin nuna wa gwamnati gazawarta kan cika sharudan da suka gindaya.
’Yan bindigar sun fara neman a biya su Naira miliyan 800 a matsayin kudin fansa, inda kwanaki uku bayan cikar wa’adin nasu suka kashe uku daga cikin daliban, kafin daga baya suka kara kashe wasu biyu.
Yanzu haka dai an kashe shida daga cikin daliban inda a Litinin din da ta gabata ’yan bindigar suka yi barazanar kashe ragowar daliban 17 muddin aka gaza cika sharadin biyan kudin fansa ta naira miliyan 100 da suka gindaya.
A dalilin haka ne Shugaban Majalisar, ya gabatar da korafi a gaban kwamitin tsaro na majalisar don ya hanzarta tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da zummar ceto daliban.
Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar, Benson Babajimi na jam’iyyar APC, ya ce Iyayen daliban sun yanke shawarar cewa ba za su bari majalisar ta sarara ba har sai an ceto ’ya’yansu.