✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nemi gwamnati ta samar da Hukumar Kula da Makiyaya

Sakamakon rikice-rikicen da ake alaƙantawa da Fulani makiyaya a Najeriya, masu ruwa-da-tsaki a harkar kiwo sun bai wa Gwamnatin Shugaba Buhari shawarwari da hanyoyin da…

Sakamakon rikice-rikicen da ake alaƙantawa da Fulani makiyaya a Najeriya, masu ruwa-da-tsaki a harkar kiwo sun bai wa Gwamnatin Shugaba Buhari shawarwari da hanyoyin da ya kamata a bi domin magance matsalar.

Sarkin Fulanin Shagamu a Jihar Ogun, Alhaji Salisu Bashankai, ya ce bai wa  harkar kiwo kulawa ta musamman ne matakin da ya kamata Gwamnatin Tarayya ta bi domin magance rikicin. Ya ce sana’ar kiwo da Fulani makiyaya ke yi na bayar da gudunmawa ƙwarai da gaske ta fuskar bunƙasa tattalin arzikin ƙasa a matakan ƙananan hukumumi da jihohi da ƙasa baki ɗaya, baya ga dimbin ayyukan yi da kiwon ke samarwa tun daga kan masu kiwon zuwa masu dakonta da ’yan kasuwa da tarin mahauta da suke dogaro a kanta.

“Don haka ya kamata Shugaba Buhari ya ƙirƙiro ma’aikata ta musamman da za ta rika kulawa da sha’anin kiwo da abin da ya shafi rayuwar makiyaya. Idan aka samar da masu taimaka wa Shugaba Buhari a sha’anin kiwo, waɗanda su ma Fulani ne da za su rika shiga lungu da saƙo suna samun Fulani makiyaya suna zama da su da yawun gwamnati, hakan hanya ce da za ta samar da maslaha,” inji shi. 

Sarkin Fulanin na Shagamu ya ƙara da cewa a yanzu an bar Fulani makiyaya suna yin rayuwar kara-zube, ba su amfanuwa da tsare-tsaren ba da ilimi na gwamnati, ’ya’yan makiyaya suna rayuwa a dazuka babu ilimin addini bare na boko, don haka dole ne a rika samun matsaloli domin jahilci ya fi hauka muni, don haka dole ne gwamnati ta sauya daga yin watsi da sha’anin kiwo da Fulani makiyaya. “Kamata ya yi gwamnati ta zamo tana da wakilai da za su rika sanya idanu a kan karatun ’ya’yan makiyaya. Wannan shi ne zai sanya a samu sauƙin sauyi a rayuwarsu, wanda zai yi daidai da ci gaban ƙasa, amma muddin aka ci gaba da yin watsi da su za a ci gaba da samun matsala, domin a yanzu za ka ga da yawa daga ’ya’yan makiyaya ba abin da suka sani sai shaye-shaye da jahilci a haka dole a rika samun matsala,” inji shi.

Ya ce akwai buƙatar gwamnati ta yi kyakkyawan bincike game da rikicin Benuwai da Taraba da ake alaƙantawa da Fulani makiyaya, domin wadansu ’yan ta’adda na iya fakewa da Fulani su yi ta’adi da nufin haifar da tarzoma da ɓata wannan gwamnati, wacce ake ganin shugabanta Bafillatani ne.