A ranar Asabar da ta gabata ne Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III ya nada Alhaji Abdulrahim Jima Alao a matsayin Sarkin Jihar Yarbawan Gombe, lamarin da ya kawo karshen ce-ce-ku-cen da al’ummar Yarbawan Jihar suka jima suna yi kan wanda zai zame Sarkinsu.
Bikin nadin wanda ya gudana a fadar Sarkin Gombe ya samu halartar mutane da dama musamman kabilar Yarbawa.
A lokacin nadin, Mista Gabriel Adelaja ne ya yi jawabi a madadin daukacin al’ummar Yarbawan jihar, inda ya gode wa Sarkin Gombe bisa wannan karamci da ya nuna musu na nada musu sabon Sarkin da suka zaba don ya jagorance su saboda a kawo karshen rikicin da ke tsakanin masu neman sarautar.
Mista Adelaja, ya kuma gode wa jama’ar Yarbawa da suka zo daga nesa da kusa suka ba da hadin kai da goyon baya wajen ganin an yi wankar sarautar sabon sarkin nasu a karo na farko a fadar Sarkin Gombe.
Mista Gabriel Adelaja daya daga cikin dattijan kabilar Yarbawa da aka haife su a garin Gombe sama da shekara 60, shi ne ya bai wa sabon Sarkin sanda a gaban Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu.
Bayan kammala nadin Mai martaba Sarkin Gombe ya ba da dawakin da suka yi wa sabon Sarkin Yarbawan Abdulrahim Alao rakiya zuwa gidansa da ke Unguwar Checheniya a garin Gombe, sannan da yamma fadar ta ba da dawaki 40 suka taya sabon Sarkin Hawan Daba da aka shirya masa a kofar Fadar Gombe don nuna jin dadi kan yadda ake zaman lafiya da al’ummar Yarbawa a jihar.
Bikin ya samu halartar Sarakunan Yarbawan da ke makwabtaka da Sarkin Yarbawan Maiduguri kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Yarbawa ta Arewa wanda wan sabon Sarkin Yarbawan Gombe ne.