An nada Alhaji Jibrin Muhammadu da akafi sani da Koturu a matsayin sabon Ardon garin Kwara da ke yankin rayawar Giza a karamar Hukumar Keana a Jihar Nasarawa.
A jawabin mai martaba Sarkin Kwara Alhaji Ibrahim Obushi jim kadan bayan ya nada shi a matsayin, ya ce an yi hakan ne bayan an yi la’akari da muhimmar gudumawa da ya dade yana bayar wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya tsakanin al’ummar Fulani da sauran kabilu daban-daban da ke yankin.
Daga nan ya bukaci sabon ardon ya yi amfani da sabon mukaminsa wajen ci gaba da hada kan al’ummar Fulani a garin Kwara da jihar baki daya. Ya kara da cewa nadin sabon ardon ya zo dai dai idan aka yi la’akari da yadda ake matukar neman hanyoyin warware rigirgimu tsakanin musamman manoma da makiyaya Fulani a yankin dama jihar baki daya, inda ya bukaci al’ummar Fulani a yankin baki daya da su bashi hadin kai don ya samu gudanar da shugabanci na gari.
Shi ma da yake jawabi Sarkin Keana Emmanuel Elayo ya yaba wa sabon ardon dangane da kyawawan halayensa wadanda a cewarsa su ne suka sa aka nada masa mukamin. Daga nan ya bukaceshi ya tabbatar ya yi duk mai yiwuwa don kawo karshen tashin-tashina tsakanin al’ummmar Fulani da sauran kabilun jihar baki daya.
Ya kuma tabbatar masa cewa a shirye masaurantar Keana take ta hada hannu da shi da sauran ardodi a yankin don tabbatar da ci gaban garin Kwara dama karamar hukumar Obi baki daya musamman a bangaren zaman lafiya, inda ya yi addu’ar Allah Ya taya shi riko.
Sauran manyan baki da suka halarci bikin sun hada da Sabon Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders a Jihar Alhaji Hussaini Muhammed da wakilin mai martaba Sarkin Kwandare Alhaji Muhammadu Al-Makura da wakilan gwamnatin jihar da sarakunan gargajiya daga ciki da wajen jihar da kuma kungiyoyi daban-daban.
An nada sabon ardon garin Kwara a Nasarawa
An nada Alhaji Jibrin Muhammadu da akafi sani da Koturu a matsayin sabon Ardon garin Kwara da ke yankin rayawar Giza a karamar Hukumar Keana…