Tauraron dan wasan Argentina da PSG, Lionel Messi, ya zama Jakadan Yawon Bude Idanu da Shakatawa na kasar Saudiyya.
Ministan Yawon Bude Idanu da Shakatawa na Saudiyya, Ahmed Al-Khateeb ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
- Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya zama shugaban PDP na Arewa maso Yamma
- Hanifa: Budurwar Abdulmalik Tanko ta ba da shaida a kotu
Messi ya samu kyakkyawar tarba a lokacin da ya isa filin jirgin saman Sarki Abdulziz da ke Jidda a ranar Litinin.
Dan wasan kwallon kafar ya samu rakiyar takwaransa Leonardo Paredes, dan wasan tsakiya na kungiyar Paris Saint-Germain da sauran abokansa.
Da yake maraba da zuwan Messi, a shafinsa na Twitter, ministan yawon bude idanun ya ce, “A yau muna maraba da zuwan Lionel Messi da abokansa zuwa Saudiyya.
“Muna taya ka murnar cewa za ka ga dumbin dukiyar da ke jibge a Bahar Maliya da kuma kayayyakin tarihin da ke kasarmu.
“Ba wannan ne zuwansa na farko ba, kuma ba shi ne na karshe ba, sannan ina farin cikin sanar da cewa a yanzu Messi ya zama jakadan yawon bude idanu da shakatawa a Ma’aikatar Yawon Bude Idanu ta Saudiyya.”
BBC ya ruwaito wanann ne dai karo na hudu da Messi ya kai ziyara Saudiyya bayan da ya jagoranci kasarsa a wani wasan sada zumunta da ta buga da Saudiyya wanda aka fafata a filin wasa na Sarki Fahd da ke Riyadh a shekarar 2011.