Mai martaba Sarkin Jama’a da ke Kudancin Jihar Kaduna, Alhaji Muhammadu Isa Muhammad II (CON) ya nada Hajiya Maimuna Abdullahi a matsayin Uwar Marayun masarautar Jama’a ta farko.
A lokacin da yake gabatar da jawabi, Sarkin Jama’a, wanda Wakilin Gabas, Alhaji Ibrahim danjaki ya wakilta ya ce wannan baiwar Allah ta samu wannan sarauta ce saboda sadaukarwarta wajen tallafa wa marayu da marasa galihu a garin Kafanchan da sauran wurare.
Malaman da suka gabatar da jawabi a kofar gidanta da ke Layin Jos a garin Kafanchan bayan kammala nadin, Sheikh Aminu kasim da Malam Nuhu Mai Ashafa sun bayyana muhimmancin tallafa wa marayu a addinin Musulunci.
Malam Aminu kassim, ya bayyana Hajiya Maimuna a matsayin wacce ta yi gadon taimako daga iyayenta. “daya daga cikin manyan ayyukan da kan janyo wa mutum samun rahamar Allah shi ne tallafa wa marayu domin su ma su ji tamkar ba su rasa iyayensu ba. Duk wanda yake so Allah Ya jikan bayansa ya kula da abin da ya bari, to shi ma ya jikan ’ya’yan wadansu ta hanyar tallafa wa rayuwarsu.”
Malam Nuhu Mai Ashafa, ya yi fatan alheri ne gare ta tare da yin kira ga sauran masu halin taimakawa su kula da marayu domin samun falalar da ke tattare da hakan.
Makada da maroka sun baje kolinsu a wajen.
Da take amsa tambayoyin Aminiya bayan kammala bikin, Hajiya Maimuna Abdullahi, ta nuna godiyarta ga Allah da wannan matsayi da Ya ba ta.
“Na dade ina taimaka wa marayu da marasa karfi ba tare da tunanin zan zama wata ba, sai ga shi aikin alherin da nake yi ya kai ga nada ni Uwar Marayu ta farko a masarautar Jama’a,” inji ta. Sai ta yi alkawarin rike amanar da aka ba ta tare da kare martabar sarautar da kuma Masarautar Jama’a gaba daya.
A karshe ta mika godiyarta ga Mai martaba Sarkin Jama’a bisa ganin dacewarta da ya yi da wannan sarautar, da kuma godiya ga maigidanta da sauran jama’ar da suka halarci bikin.
Babban Limamin Juma’a na Kafanchan, Sheikh Adamu Tahir ne ya rufe taron da addu’a.