Idan ka ji tambura sai fada, inji ‘yan magana, ai kuwa haka ne, domin a makon jiya ne fadar sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ta cika da tambura da busar algaita da kuma cincirindon jama’a don halartar bikin nadin Magajiyar ’Yan Sarkin Kano, Hajiya Fatima Ado Bayero. Wannan shi ne karo na farko da aka yi bikin nadin sarautar ‘Magajiyar ’Yan Sarki’ a shekara 60 da ta gabata. Bayan bikin ne Aminiya ta tattauna da Magajiyar inda ta ba da tarihinta da kuma nuna jin dadinta. A karshe ta ba mata shawara su nemi ilimi su kuma kama sana’a.
A ranar Lahadi 19 wannan watan ne Masarautar Kano ta gudanar da bikin nada Hajiya Fatima Ado Bayero wacce aka fi sani da (Ya Balaraba) sarautar Magajiyar ‘Yan Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
Wannan shi ne karo na farko da aka sake bikin nada wannan sarautar bayan da aka shafe shekara 60, wato tun lokacin Sarki Abdullahi Bayero ba a nada ba.
An gudanar da bikin a fadar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, inda ‘yan uwa da abokan arziki suka taru don taya Magajiyar murna.
Wani dan Sarkin Kano, Yarima Umaru Ado Bayero, ya yi wa Aminiya karin haske game da sarautar Magajiyar ‘Yan Sarki inda ya ce, tsohuwar sarauta ce mai dadadden tarihi, “wacce ta samo asali daga lokacin mulkin Sarki Alu, inda sarakunan ke nada babbar ‘yarsu mace a wannan sarauta da nufin ta kara kulla zumunci tsakanin ‘ya’yan sarki da kuma sulhunta tsakaninsu. “ Inji shi.
Hajiya Gwaggo Ado Bayero ‘yar uwar magajiyar ta bayyana farin cikinta game da wannan sarauta da aka yi wa ‘yar uwarta.
Ta ce: “Na yi farin ciki matuka da aka nada ‘yar uwata wannan sarauta, ba zan manta ba mun taso mun yi wayon sanin yayar mahaifinmu sarki wacce ke da wannan sarauta ana kiranta Gwaggo Magajiya, sai dai tun daga kanta ba a sake nada wannan sarauta ba sai a yanzu da aka nada ‘yar uwarmu.”
Aminiya ta tattauna da Magajiyar ‘Yan Sarki Hajiya Fatima Ado Bayero jim kadan bayan nadin da aka yi mata, inda ta bayyana cewa ta yi farin ciki da wannan nadin sarauta da aka yi mata tare da fatan Allah Ya yi mata jagora.
Ta ce: “Na yi farin ciki da murna kwarai da gaske game da wannan sarauta da aka yi mini. Ina kuma alfahari da iyayena da ’yan uwana da suka ga dacewata da wannan sarauta. Ina addu’ar Allah Ya taya ni riko.”
Hajiya Fatima ita ce babbar ‘yar Sarkin Kano Ado Bayero ta gutsura wa Aminiya kadan daga tarihin rayuwarta inda ta ce an haife ta a shekarar 1957. Ta fara karatun firamare a kasar Senegal a lokacin tana hannun marikiyarta Hajiya Dudu wacce kanwar Sarkin Kano, kuma matar Ambassada Sani Kwantagora ce. “Lokacin da muka je kasar Senegal da marikana sai aka sanya ni a makaranta a can. Kasancewar a Senegal da harshen Farasanci ake koyarwa, na ci gaba da karatu har zuwa aji biyu na firamare, daga nan sai aka ga dacewar na dawo gida Najeriya domin na koyi harshen Turanci, don haka sai aka kai ni makarantar firamaren Shekara inda na karasa karatuna a can. Bayan na kammala sai na shiga makarantar Sakandire ta GGC Dala. Ina aji uku sai aka cire ni aka yi min aure da dan uwana Ambassada Mahmud Sanusi.
“Sai dai a wancan lokacin duk da cewar ina karatu a Kano, bai sa na koma hannun iyayena ba, da zarar mun sami hutun makaranta sai na koma can wurin marikana wanda su kuma ba sa zama a kasar nan. Kafin lokacin da aka yi min aure ba na mantawa mun zauna a kasashen Senegal da Nijar da Murtaniya da kuma Saudiyya” Inji ta.
Hajiya Fatima ta kara da cewa yin aurenta ya kara ba ta damar zagaya duniya da sanin al’adu mabanbanta “Kasancewar na auri dan uwana wanda yake shi ma jakada ne, sai hakan ya ba ni damar zagaya duniya, inda na hadu da mabambantan al’adu. Da farko mun fara zama a Japan, sannan muka je Jamus da Iran da Amurka da Ingila. A Afrika kuma mun zauna a Zambiya. Kafin rasuwarsa mun haifi ‘ya’ya hudu tare da shi kuma a hannunsa na karasa karatuna. A yanzu haka ina auren dankadan Kano Hakimin T/Wada Dokta Bashir Ibrahim”
Game da nadin da aka yi mata Hajiya Fatima ta ce “ayyukan da aka dora min ba wani sabon aiki ne daban da muka saba gudanarwa a matsayinmu na ‘ya’ya mata ba. Dama mu a gidanmu an yi mana tarbiyyar zumunci da son ‘yan uwanmu, duk da cewar ba za a rasa wani abu can da nan ba. Mu a gidanmu ba mu san wariya ba, kasancewar gidanmu babba ne, ba ya ga mu ’ya’yan sarki akwai sauran jama’a a gidan. Babu damar da za a ce mu ’ya’yan sarki kadai ne za mu yi hulda da junamu.
“Abin da aka nuna mana shi ne duk wanda muka gani a gidanmu dan uwanmu ne. Kuma dole ne mu girmama shi idan ya girme mu. Koda ya kasance sarki zai yi mana kyauta, idan muka taru zai fara da manyan cikinmu, sannan a gangaro har zuwa kasa. Babu kuma wariya tsakanin ‘ya’yansa da sauran mazauna cikin gida. A yanzu ma da aka ba ni wannan sarauta a kan hakan zan ci gaba in sha Allah wajen kara kulla zumuncin da ke tsakaninmu tare da sulhunta junanmu yayin da aka sami sabani.” Inji Magajiya.
A karshe ta yi kira ga mata da su nemi ilimi tare da neman sana’a. “Ina kiran mata da su nemi ilimi. Haka kuma ina ganin akwai dacewar a ce kowace mace ta sami abin yi domin a kalla za ta taimaka wa kanta da iyalinta da dan abin da take samu daga sana’arta”.
Adam Umar, Abuja
Wata mata mai suna A’isha Ambursa ta gudu bayan an zarge ta da ta kwara wa makwabciyarta Bukki Sharif ruwan zafi.
Al’amarin ya faru ne Litinin da ta gabata a unguwar Afo da ke garin Suleja a Jihar Neja sakamakon kawo ruwan famfo, inda wadda ta kona da wadda aka kona din suka yi sa-in-sa a kan fara diban ruwa.
Kodayake an ce ba wannan ne lokaci na farko da suka fara sa-in-sar ba, da ma akwai rashin jituwa tsakaninsu wadda ‘ya’yan da suka haifa suka zama sila.
’Yan sanda a garin Suleja sun ce suna neman A’isha sakamakon zargin da ake yi mata na kona wata makwabciyarta mai suna Bukki Sharif da suke haya a gida daya.
Wakilinmu ya zanta da wadda aka kona mai suna Bukki Sharif ’yar asalin garin Isafa da ke Jihar Kwara, wadda kuma take zaune a Unguwar Afo a Suleja, inda ta ce al’amarin ya faru ne bayan an kawo ruwan famfo a ranar Litinin da ta gabata, a lokacin ita da sauran matan da ke haya a gidan sun yi layin diban ruwa, “a daidai lokacin da layi ya iso kaina sai A’isha Ambursa ta hana ni diban ruwa bayan ta saka abin diban ruwanta a gaban nawa, sai na ce mata na riga ta amma sai ta ce idan ina da karfi sai na hana ta.“Bayan na bar wurin sai na nufo dakina, sai ta biyo ni sannan ta kwada mini tukunya inda a nan muka fara fada, daga bisani makwabta suka raba mu.” Inji Bukki.
Bukki ta zargi A’isha da shake wuyar danta dan wata takwas, sai dai ta ce wata makwabciyarsu mai suna Chineye ce ta kwace shi daga hanunta sannan ta gudu da jaririn a matsayin kariya. Ta ce “Daga baya na sake koma wa wurin diban ruwa, a nan ne kuma ta nufo kaina ta watsa min ruwan zafi. makwabta sun kama ta amma sai ta sulale gabanin kai maganar wajen ’yan sanda.”
Mijin wadda ake zargin mai suna Faruku Bello ya ce ya samu labarin faruwar al’amarin ne a lokacin da yake wani wuri, amma ya garzayo gida a lokacin. Ya ce shi da matarsa ’yan asalin Jihar Kebbi ne, ya yi ikirarin bai san inda matarsa take ba a halin yanzu, “Na buga waya gida Birnin Kebbi, amma sun ce ba ta je gida ba.”
Ya dangata al’amarin da rashin jituwa da ke tsakanin matarsa da wadda ake zargin ta kona din a kan dansa mai shekara 3, wanda matarsa ke zargin na tsangwamarta da jaririnta a gidan da suke hayar, sannan idan ta kai kara wajen mahaifiyarsa ba ta yi masa komai, inda ya ce sha’ani ne na yara.
“Zan ba da hadin kai ga mijin matar da aka kona din, wajen jinyarta wadda a yanzu haka aka kai ta wajen wani malami da ke yi mata addu’o’i a Suleja.” Y ace daga karshe.
Shi ma a ganawarsa da Wakilinmu, mijin matar da aka kona mai suna Sharif Olayigo, ya ce tun bayan aukuwan lamarin dansu mai wata 8 ba ya iya samun tsotson nonon mahaifiyarsa kasancewar nono na yi mata ciwo a duk lokacin da zai yi tsotso.
Mai Unguwar Afo ta gabas, Malam Bello Dandin Mahe, ya bukaci mata musamman da ke zaune a gidajen haya da su rika hakuri da junansu don magance aukuwar al’amarin irin haka.
Babbar jami’ar ’yan sanda (DPO) ta A dibision a Suleja ta shaida wa Wakilinmu cewa, bayan aukuwan lamarin a ranar Litinin da ta gabata an garzayo da wadda aka kona din mai suna Bukki Sharif ofis dinsu, inda mijinta mai suna Sharif Olayigo ya shigar da kara, kuma tun a wancan lokacin ne suke neman wadda ake zargin, kasancewar ta tsere bayan aikata abin da a ke zarginta da aikatawa.