✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada kanin Kwankwaso sarautar Makaman Karaye

Ganduje: Sarki ke da ikon nada Hakimin Karaye ga Gwamna ba.

Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II ya nada kanin tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Kwankwaso, wato Alhaji Saleh Musa Saleh Kwankwaso (Baba), a matsayin sabon Makaman Karaye kuma Hakimin Madobi.

Sarkin Karaye ya kuma tabbatar da Alhaji Saleh Musa Saleh Kwankwaso, a matsayin daya daga cikin Masu Zabar Sarki a zaman da ta yi ranar Laraba, 13 ga watan Janairu, 2021.

Ba da sarautun, wadanda mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso ya rasu a kai, na zuwa ne kasa da mako uku bayan rasuwar mahaifin nasa a ranar 25 ga Disamba, 2020.

Jami’in Yada Labaran Masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa, ya ce Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II ya shawarci sabon Makaman na Karaye da ya yi koyi da kyawawan dabi’un mahaifinsa na dattaku, son jama’a, zaman lafiya, sadukar da kai ga al’ummarsa da kuma da’a ga Masarautar.

Ganduje zai nada Makaman Karaye

Nadin na zuwa ne kasa da mako daya bayan Gwamnan Kano Adullahi Ganduje, wanda ba ya ga-maci da Sanata Kwankwaso, ya ba da tabbacin barin sarautar a gidan nasu Kwankwason.

Ganduje ya ba da tabbacin ne a lokacin da ya ziyarci gidan marigayin domin gaisuwar ta’aziyya ga Sabon Makaman Karayen, wanda ya kasance wakilin mahaifinsa na sama da shekara 20 a ayyukan sarautun da ya rike kafin Allah Ya yi masa rasuwa.

An haifi Alhaji Saleh ne a shekarar 1964 kuma yana da shaidar karatu ta Diploma a fannin Injiniyan Gine-gine.

Tabbacin da Ganduje ya bayar na ba da Sarautar ga kanin na Sanata Kwankwaso, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce, Aminiya ta jiyo ta bakin masana da masu kusanci da lamarin.

Sarki ke da ikon nadin Makaman Karaye ba Gwamna ba

Dokta Tijjani Naniya masanin tarihi ne a Jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana cewa nadin masu zabar sarki da hakimai da wasu sarautu hakki ne na masarauta – ma’ana sarki ne ke da cikakken iko akan hakan amma ba gwamna ba.

“Idan mun duba a tsarin sarautun gargajiya akwai sarautun da suke na gado ne da kuma wadanda sarki ne kadai yake zabo mutane ya dora su akwai kuma sarautun da na ’ya’yan sarki ne.

Sai dai alfarma

A duk wadannan sarautu, sarki yana bayar da sarautun ne ga wadanda yake jin za su zauna lafiya su yi aiki tare.

A cewarsa, babu wanda ya isa ya dauki sarautar ya nada wani, sai dai bisa neman alfarma.

“Idan wani mutum ko Gwamna yana son a nada wani sarauta zai iya zuwa gaban sarki ya nemi alfarma don a yi wa wanda yake son sarautar.

“Hakan ta taba faruwa lokacin da marigayi Gwamnan Kano Alhaji Abubakar Rimi, ya taba zuwa gaban Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya nemi alfarmar don a nada dan uwansa sarautar Dagaci wanda kuma aka yi masa wannan alfarma.”

Tasirinsa ga siyasar Kwankwaso da Ganduje

Farfesa Kamilu Sani Fagge masanin harkar siyasa ne daga Jami’ar Bayero, ya bayyana cewa nadin da Gwamna Ganduje ke batun yi wa kanin Sanata Rabi’u Kwankwaso zai yi tasiri a siyasance ta fuskoki guda hudu da suka hada da raguwar kiyayya tsakanin bangrorin biyu da kuma kara wa Gwamnan Ganduje farin jini da karbuwa a wurin jama’ar Jihar.

A cewarsa duk da cewar ba wani sabon abu ba ne don an dauki sarauta an mayar da ita gidan da ta fito, amma a wannan karon lamarin ya sha bamban, duba da irin rashin jituwar da ke tsakanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Gwamnan na Kano wanda wasu ke tunanin cewa Gwamnan zai iya dauke ta daga gidansu Kwankwason ya kai ta wani wuri.

“Kamar yadda kowa ya sani idan basarake ya rasu akan dauko daya daga cikin ’ya’yansa a ba shi wannan sarauta. An saba ganin hakan.

“Amma idan mun duba a siyasance idan har Gwamna ya ba kanin Sanata Kwankwaso sarautar hakan, zai yi tasiri matuka domin na daya lamarin zai iya rage rashin jituwar da ke tsakanin Gwamnan da kuma Sanata kwankwaso.

“Haka kuma lamarin zai kara wa Gwamnan karbuwa a wurin jama’a domin za a ga cewar ya yi dattaku bai yi amfani da siyasa ba.

“Watakila kuma shi wanda aka nada din duba da cewa yana da alaka da bangarorin biyu zai iya amfani da damarsa wajen sulhunta mutanen biyu wato yayansa Kwankwaso da kuma gwamna Gnaduje idan har su manyan sun sauko daga dokin zuciya.

“Haka kuma abin zai rage matsalar tashe-tashen hankali a tsakanin al’umma, domin idan Ganduje ya ce zai dauke sarautar daga gidansu Kwankwaso, ya zama cewa magoya bayansa su ki amincewa da hakan wanda zai kai ga tayar da hankali da sauransu,” inji shi.