An nada tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan a matsayin Uban Jami’ar Cavendish ta Kasar Uganda (CUU).
Hakan na kunshe cikin wani sako da jami’ar ta wallafa a shafinta na Facebook a wannan mako, inda ta bayyana farin cikin samun sabon shugaba tare da yi masa fatan samun nasara wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Wani rahoto da Muryar Amurka VOA ta wallafa, ya ce mukamin na Uban Jami’a wanda a yaren Ingilishi ake kira da ‘Chancellor’ na jami’ar ta CUU da ke kasar Uganda, na daya daga cikin muhimman karamci na kasa-da-kasa da tsohon shugaban na Najeriya ya samu tun bayan saukarsa daga mulki a shekarar 2015.
Jami’ar ta Cavendish mai zaman kanta wacce aka bude a shekarar 2008, na daya daga cikin manyan jami’o’i a nahiyyar Afirka.
Alkaluma na tarihi sun ce jami’ar ta soma gudanar da ayyukanta a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kasar Zambia, Marigayi Kenneth Kaunda, wanda ke matsayin Uban Jami’ar
Jami’ar CUU na da hadin gwiwa da Kwalejin Cavendish da ke birnin Landan da sauran cibiyoyinta na jami’o’in Cavendish da ke kasashen Tanzania da Zambia, inda ta soma yaye dalibai a shekarar 2011.