Dagacin Unguwar Madaki da ke yankin Bolari a Jihar Gombe Alhaji Atiku Marafa, ya nada Hajiya Hauwa Muhammad Alkyabbar Matan Unguwar Madaki ta farko.
Hajiya Hauwa Muhammad wadda aka fi sani da Adda Laddo, an haife ta ce a ranar 6 ga Disamban 973 a Karamar Hukumar Bayo a Jihar Borno, kuma tun tana da shekara bakwai aka sa ta a makarantar allo.
A lokacin da ta kai shekara goma ne ta fara kasuwanci kuma da ta kai shekara 13 sai aka yi mata aure da Malam Muhammad Jambi Lamba.
Ganin kwazonta wajen taimakon al’umma ne, Dagacin Madaki ta Arewa Alhaji Atiku Marafa ya nada ta Alkyabbar Matan Unguwar Madaki ta Arewa ta farko.
Da yake jawabi Dagacin Madaki Alhaji Atiku Marafa, ya ce nadin da ya yi wa Hajiya Hauwa Muhammad a matsayin Alkyabbar Matan Madaki ta Arewa ya zo a lokacin da ya dace.
Dgacin ya ce Hajiya Hauwa ’yar gida ce domin ta zauna a cikin gidan Marafa, tare da mijinta na tsawon shekara biyu kafin su fita kuma tana taimaka wa al’umma hakan yasa ya nada ta Alkyabbar Matan Madaki don ta ci gaba da gudanar da ayyukan da ta saba.
Daga nan sai ya yi mata addu’a da fatar Allah ya ba ta ikon sauke nauyin da ke kanta.
Da take jawabin godiya Alkyabbar Matan Madaki, Adda Laddo, gode wa Hakimin Bolari ta yi wanda da amincewarsa ce Dagacin ya nada ta.
Ta kuma gode wa Dagacin Madaki da ’yan majalisarsa domin da amincewarsu ne aka ba ta wannan sarauta.