Mai martaba Sarkin Piriga da ke Karamar Hukumar Lere, a Jihar Kaduna Mista Jonathan Zamuna ya nada Alhaji Suleiman Maigamo Dee Idris a matsayin Sabon Dagacin Gurza. Sarkin ya yi wannan nadi ne a fadarsa da ke garin Gure a karshen makon jiya.
Da yake jawabi a wajen nadin, Sarkin Piriga Mista Jonathan Zamuna ya ce an nada Alhaji Suleiman Maigamo sabon Dagacin Gurza ne saboda ganin cancantarsa da irin gudunmawar da yake bayarwa, wajen ci gaban Masarautar Piriga.
Ya yi kira ga sabon Dagacin ya rike wannan amana da aka damka masa tsakani da Allah ta hanyar rike jama’arsa da gaskiya da rikon amana, domin ganin an ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, a tsakanin al’ummarsa da al’umomin masarautar baki daya.
Har ila yau ya yi kira ga sabon Dagacin ya taimaka kan abubuwan da suka shafi sha’anin tsaro, ta hanyar kai rahoton duk wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautar.
Da yake zantawa da Aminiya bayan kammala nadin, sabon Dagacin Gurza Alhaji Suleiman Maigamo Dee Idris ya ce babu abin da za ce, kan wannan nadi da aka yi masa, sai dai ya yi wa Allah godiya.
“A rayuwata ban taba tsammanin cewa zan zama Dagacin wannan kasa ta Gurza ba. Na gaji wannan sarauta ce daga wajen mahaifina, wanda ya ce ya gaji da sarauta, saboda yanzu yana da shekara 110 a duniya. An nada mahaifina Dagacin wannan kasa ta Gurza ce tun ranar 27 ga Oktoban 1970, a fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya, kuma shi ne Dagacin Gurza har zuwa lokacin da aka nada ni kan sarautar.
Sabon Dagacin ya roki Allah Ya ba shi ikon rike jama’ar wannan yankin cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya kamar yadda mahaifinsa ya yi shekara 48 yana yi.
Ya yi kira ga al’ummomin yankin da suka hada da Kurama da Fulani da Hausawa da Amawa da Fiti da Janji da sauransu su ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Domin zaman lafiya ne zai kawo ci gaba a yankin da jihar da kasa baki daya.
Ya yi kira ga wadanda suka yi takarar sarautar su ba shi goyon baya da hadin kai, su hada hannu domin su kawo ci gaba ga yankin.
Daga nan ya mika godiyarsa ga Mai martaba Sarkin Piriga da Mai girma Hakimin Gundumar Garu kan wannan nadi da aka yi masa.