Shugaban Karamar Hukumar Chibok a jihar Borno, Umar Ibrahim Hauri ya mika ’yan mata 18 da aka ceto ga iyalansu a karshen mako.
10 daga ciki cikin wadanda ake ceto ’yan garin Chibok ne, sauran takwas kuma an sace su ne daga Unguwar Pemi ta karamar hukumar.
- 2023: Bangaren Wike ya fice daga kwamitin yakin neman zaben Atiku
- Buhari zai ciyo bashin N402bn domin biyan bashi
- DAGA LARABA: Tashin Hankalin Da Samari Ke Ciki Amma Suke Boyewa
Hon. Hauri ya ce Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya amince a fitar da kudi Naira miliyan 1.4 da tallafin abinci ga wadanda abin ya shafa ta hannun Ma’aikatar Harkokin Mata da Cigaban Jama’a.
Kowacce daga cikin ’yan matan Chibok 10 ta samu kudi Naira 100,000 da kayan abinci, yayin da sauran takwas da aka sace a unguwar Pemi aka ba su Naira 50,000, da kayan abinci kowaccensu.
Shugaban, a lokacin da yake gabatar da kayayyakin, ya gode wa Gwamna Zulum bisa tallafin da ya ba su, ya kuma bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da su yadda ya kamata.
Wadanda suka halarci bikin mika kudaden da kayayyakin tallafin sun hada da mataimakin shugaban karamar hulumar, sakataren karamar hukumar, kansiloli, shugabannin gargajiya, masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC, shugabannin mata da dai sauransu.