Gidajen marayun Musulmi da na Kirista a Gombe ya koka kan rashin tunawa da marayunsu a rabon tallafin abincin da Gwamnatin Tarayya ta bayar a raba wa masu karamin karfi a jihar.
Shugaban gidan marayun Musulmi a jihar, Dokta Babayo Kolo, ya shaida wa Aminiya cewa gwamnati ba ta ware kudade ko wasu kayan abinci na musamman da take bayarwa domin gidan marayun ba.
Kolo ya ce gidan yana da yara masu yawa amma da yake sun girma sun wuce zama a gidan sun sallame su suka kawo wasu kanana da suke tsakanin shekaru 4 zuwa 12.
Hakazalika, Babban Daraktan gidan marayu na Kirista (Christian Covenant & Orphans Foundation) a jihar, El-Polycarp Y Degri, ya ce ba su taba samun tallafin kayan abincin palliative da gwamanti ta raba a jihar ba.
El-Polycarp, wanda shi ne Babban Sakataren gidajen marayu na Kiristoci na Najeriya, ya shaida wa wakilinmu hakan ne a lokacin da wasu mata ’yan sanda a jihar suka kai wa gidajen marayun biyu tallalfin kayan abinci da sauran kayan masarufi.
Ya ce daidaikun jama’a da kungiyoyi ne kadai suke ziyartar gidan marayun su tallafa musu domin yaran su samu abin da za su ci da sutura, ba daga gwamnati ba.
El-Polycarp Degri, ya yaba wa kokarin mata ’yan sandan da har suka tuna da marayun suka kai musu tallafin.
Ya bayyana cewa hakan ya taimaka, domin ana cikin nawuyacin halin rayuwa.
Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Gombe da ta tarayya da su dube su wajen kulawa da gidajen marayu saboda marayun suna matukar bukatar tallafi.
Da Aminiya ta tuntubi shugaban kwamitin rabon kayan tallafin na jihar Gombe wanda kuma shi ne shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar (SEMA) Abdullahi Haruna, kan batun sai ya ce shi bai ma san akwai gidajen marayu na kirista a jihar ba.
Amma ya san da na Musulmi kuma ya taba zuwa sau daya ya kai musu tallafi daga ofishinsa na SEMA.
Sannan ya ce bayan sun gama rabon kayan abincin wasu gidajen marayu sun rubuta musu takardar neman tallafi idan aka kawo kayan abinci na Gwamnatin Tarayya kuma idan aka samu din za su ga yadda za su yi su tallafa musu.