An maka surukin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda kuma ya nemi takarar Gwamnan Kaduna a jam’iyyar APC, Alhaji Sani Muhammad Sha’aban a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Zariya, saboda taurin bashi.
Ana dai zargin Sani Sha’aban ne da kin biyan bashin kudaden da suka kai Dalar Amurka miliyan daya, da kuma kudin Najeriya Naira miliyan 11 da dubu 200 da ya ranta shekaru hudu da suka gabata.
- Babu wanda zai sake cire sama da N20,000 a rana daya a POS – CBN
- Fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna na neman diyya daga Buhari
Mai kara, Umar Faruk Abdullahi ta hannun lauyansa, Usman Kuso ya roki kotun da ta bayar da umarni domin a sayar da kadarorin wadda ake kara domin a biya bashin da ya ci, kuma ya ki biya.
Mai karar ya kuma ce idan an sayar da kadarorin amma kudin ba su cika ba, a kuma sayar da wasu kamar yadda yarjejeniyar bashin ta kunsa.
Lauyan ya shedawa kotun cewar mai karar aboki ne ga wadda ake kara watau Alhaji Muhammad Sani Sha’aban.
Lauya Kuso ya shaida wa kotun cewa a wani lokaci a shekarar 2018, wanda ake karar ya je wajen mai kara a lokacin suna tare da wani abokinsu mai suna Bashir Abubakar, inda shi wadda ake kara ya bukaci da ya bashi rancen kudi har Dalar Amurka miliyan daya da kuma kudin Najeriya Naira miliyan 11 da dubu 200.
Ya ci gaba da yi wa kotu bayanin cewa wadda ake kara, ya bukaci da a samar da bayanan yadda za a biya da kuma yarjejeniya kamar yadda shari’ar musulunci ta tanada.
A cewar lauyan, wanda ya yi karar ya amince da bukatar mai karar kuma shi Muhammad Sani Sha’aban ya bukaci lauyansa, Ismaila Musa Jamoh da ya tsara takardar yarjejeniyar.
Takardar yarjejeniyar ta kunshi takardun mallakar kadarorin wadda ake kara domin a amince a bashi rancen.
Lauyan ya bayyanawa kotun cewa daga cikin kadarorin akwai gini da ke lamba 48 a layin Yusuf daura da Layin Hadeja da ke Bompai a jihar Kano mai lambar mallaka 009234, ai kuma Kamfanin Mazari Ltd wadda ke kan hanyar Kano zuwa Kaduna a Zariya mai shaidar mallaka KD 6246, Zariyan jihar Kaduna.
Sauran kaddarorin sun hada da TULIPS da ke mahadar MTD daura da titin Queen Elizabeth GRA Zariya.
Haka nan kuma akwai fili da gini a titin Circular GRA Zariya mai lambar mallaka KD 11226 da kuma wani gini da ke bayan gidansa kusa da makarantar Therbow mai lamba 3964.
Lauyan ya kuma shaida wa kotu cewa a lokacin da aka bayar da bashin, Sani Sha’aban yana Dubai, wannan ne ya sa bai sanya hannu akan takardar da kansa ba, sai lauyansa Ismail Musa Jamoh.
Shi Sha’aban ya umurci Dansa Muhammad Turad Sha’aban, wanda yake auren diyar Shugaba Buhari, ya sanya hannu a kakardan yarjejeniyar a madadinsa, hakan nan kuma sai da Kwamishina ya sanya hannu na rantsuwa wadda ke Babban Kotun jihar Kaduna, kafin aka bayar da rancen kudaden da wadda ake kara.
Lauyan ya kuma shaidama kotu cewar bayan da wanda ake kara ya dawo Najeriya ya sanya hannu da kansa a wata takardan yarjejeniyar ta daban da shi mai karar.
Ya ce, yarjejeniyar ta ginu ne akan za a biya bashin bayan wata shida, amma tun da aka bayar a shekarar 2018 bai biya ba har aka zo gaban kotun.
Da ya ke mayar da martani lauyan Muhammad Sani Sha’aban, Nasir Sa’idu ya ce babu wata alaka tsakanin mai kara da wadda ake kara a bangaren yarjejeniya, kuma yarjejeniyar da aka yi ba ta yi bayanin kokari ko ranar da aka bayar da kudaden ba ga wadda ake kara ba kuma ba a ayi bayanin yadda aka bayar da su ba.
Mai shari’a Malam Aminu Jumare ya dage sauraran karar har zuwa ranar 4 ga watan Janairu 2023, tare da shawartar bangarorin biyu da zu yi kokarin lalubo hanyar sulhu kamar yadda shari’ar musulunci ya umurta.